Malam nayi rashin lafiya kaina ya kwakuye, mijina yana bakin ciki, idan yaga kaina.
Kozan iya kara gashi, don zaman auranmu ya kara dadi ???
AMSA.
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To 'yar uwa wata mace taje wajen Annabi (s.a.w) tabashi labari cewa:
'Yarta tayi rashin lafiya gashin kanta yazube, kuma gashi mijinta ya umarceta data kara mata gashi, shin zata iya Qarawa ???.
Sai Annabi (s.a.w) yace mata:
A'a, saboda an la'anci masu Qara gashi"
Bukhari ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta:4831.
Hadisin yana nuna cewa:
Baya halatta mace taqara gashi, koda kuwa mijinta ne ya umarceta.
Saboda hakan zaisa tashiga tsinuwar Allah.
Allah shine mafi sani.