Gwamnatin kasar Syria ta ce ‘yan ta’adan IS sun kashe mutane da dama a tsohon birnin Palmyra dake tsakiyar kasar. Bayanai sun nuna cewa akalla fararen hula 400 ‘yan ta’adan suka kashe a birnin na Palmyra, da suka hada da mata da yara, bisa dalilin goyon bayan su ga shugaba Bashar Assad, da kin karbar umurni daga kungiyar ta IS. Cikin wadanda suka rasa rayukan su akwai ma'aikatan hukumomi, da na kamfanonin gwamnatin, kana akwai mutane fiye da dubu daya, wadanda kungiyar ta hana fito daga birnin na Palmyra.
Title :
Kimanin Fararen Hula 400 (IS) Ta Kashe A Birnin Palmyra Na Syria
Description : Gwamnatin kasar Syria ta ce ‘yan ta’adan IS sun kashe mutane da dama a tsohon birnin Palmyra dake tsakiyar kasar. Bayanai sun nuna cewa aka...
Rating :
5