Assalamu Alaikum, Karo na biyu kenan ina turowa, Don Allah a amsa mun wannan tambayar.
Allah ya taimaki Mallam, ya kuma kareka daga sharrin makiya, da kuma dukkan musulmai baki daya. Mallam tambaya nake dashi kamar haka: Nine nake aiki a ma'aikatar gwamnati, a karkashin wata hukuma da take shirya jarrabawa a ma'aikatan gwamnati, to a tsarin ni ina karkashin 'Director' ne, to kuma akwai 'Staff Officer wanda shine alhakin al'amuran jindadi da walwalar ma'aikata yake hannunsa, sai kuma mataimakinsa shine wanda yake da alhakin duk wani lamari na ma'aikata a wannan ofis namu, saboda iya aikinsa ya zamana duk aikin Staff Officer din shine yake yi (an danka masa komai a hannunsa), amma shi mutum ne wanda yake da son zuciya da kuma almundahana. A halin da ake ciki yanzu ya sameni akan wani mutum yayi jarrabawa kuma baici ba, akan lallai sai na gyara masa, rashin bashi hadin kai daga gurina zai iya kawo mun cikas a cikin aikina, kuma ya karbi kudi a gurin wannan mutumin masu tarin yawa da sunan zai taimake shi, to ni saboda kar ya bata mun al'amarina nayi masa abinda yake so, sai ya bini har gida ya kaimun kudi (wani abu daga cikin abin da wancan mutumun ya bashi). Na karbi kudi saboda amma banyi amfani da su ba, saboda tsoron kaucewa shubuha, shin mallam wacce irin nasiha zaka mun ni da yan'uwa musulmai akan yadda zamu gyara aikin mu, kuma shin wadannan kudin da ya bani nayi sadaka dasu gaba daya banyi amfani dasu ba, kuma ba don na samu lada ba, na niyyar na kauce ma wannan abin, shin yaya matsayin wannan abin yake.
Don Allah Mallam iyali na tana fama da mummunan hawan jini, duk lokacin da ta samu ciki to sai jininta yayi ta hawa, daga karshe har abunda yake cikin ya mutu aje asibiti a cire shi, muna rokon zauren fiqhu da sauran al'umma su taimaka da addu'a, Zauren Fiqhu kuma bayan addu'ar ya taimaka da shawara da kuma magani, don asibiti munyi iya bakin kokarin mu, don yanzu haka ma tana da juna biyu kuma mun fara sintirin zuwa asibiti.
Na gode Allah yasaka da alheri, kuma a boye sunana.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Nasihata gareka da dukkan Ma'aikatan Gwamnati ko Kampani ita ce:
* Ka sani amatsayinmu na Musulmai, duk abinda zamuyi, wajibi ne mu aunashi abisa ma'aunin shari'ar Allah. wato Alqur'ani da Sunnar Manzon Allah (saww) .
* Bai halatta Amatsayinka na musulmi ka rika Aikata duk wani abinda zai janyo maka matsala tsakaninka da Allah ba. koda kuwa abin zai burge mutane.
* Cin hanci da rashawa, HARAMUN NE bisa fahimta irin ta addinin nan namu. Harma Manzon Allah (saww) yace : "ALLAH YA TSINE MA MAI KARBAR CIN HANCI DA KUMQ MAI BAYARWA".
Cin hanci da rashawa yana daga cikin ayyukan zalunci wadanda babu irinsu. Misali yanzu kamar wannan mutumin da kuka gyara ma sakamakon jarrabawa, Watakil yaje ya nemi aiki awata ma'aikatar Gwamnatin ko kuma wani Kampani, su kuma zasu daukeshi ne abisa abinda sakamakonsa ya nuna.
Kaga kenan ta dalilinku an daukeshi aiki, kuma watakil ya chutar da al'ummah saboda rashin kwarewarsa. Watakil idan aikin likitanci ne, yaje yayi ta kashe al'ummar Annabi (saww).
Amma da yake kayi bayanin irin halin da kuke ciki awajen aikin, watakil idan ka bijire ma wannan Shugaban naku, ya haifar maka da matsalar da zata janyo makabarin wajen aikin.
Annabi (saww) yace : "ALLAH YA DAUKE MA AL'UMMATA SABODA NI, LAIFIN DA SUKA AIKATA CIKIN KUSKURE DA KUMA WANDA SUKA YI CIKIN MANTUWA, DA KUMA WANDA AKA TILASTA MUSU AKANSA".
kuma yace: "KAJI TSORON ALLAH ADUK INDA KAKE, KUMA KABI BAYAN MUMMUNAN AIKI DA KYAKYAWA, ZAI KANKARESHI".
Kaci gaba da zarginta stigfari da beman gafarar Ubangiji tare da fatan Allah ya kiyaye maka faruwar irin wannan ana gaba.
Ita kuwa matarka, ka kaita wajen likitochin Musulunci suyi mata tambayoyi. Domin watakil abun ya samu alaka da wani abinda likitocin zamani basu sani ba.
Allah ya sawwake, Allah shi bata lafiya.
WALLAHU A'ALAM.