To amma a baya bayan nan bayanan rashin biyan ‘yan kwangila sun fara fitowa fili.
Alhaji Audo Maitangaran shugaban kungiyar ‘yan kwangila ta jihar Kano yace gwamnati ce ta takalesu. Yace su da suke mua’amala da gwamnatin jihar da ma gwamnan domin su ne suke goyon bayansa bai kamata ya shiga gidan radiyo ba yana gayawa duniya cewa ‘yan kwangila basa bin gwamnatinsa bashi.Yace suna bin gwamnatinsa makudan kudi da suka samo asali tun daga gwamnatocin da suka shude.
Alhaji Maitangaran yace sun san cewa suna binsa nera miliyan dubu sittin ko N60b. Ya kara da cewa idan sun gama hada alkaluma zasu samu fiye da nera miliyan dubu dari da suke bin gwamnati. Sun samu jimillar kudin ne daga takardun shaidar cewa sun kammala ayyuka amma ba’a biya ba. Yace akwai wasu ayyuka ma da suka gama ama har yanzu takardun gamawar basu fito ba don haka irin wadannan basa cikin lissafi tukunna.
To amma da aka tunkari gwamnan ya mayarda martani sai yace gwamnatin jihar Kano bata ci bashi a kasashen waje ba ko na bankunan cikin gida Najeriya ko cin bashin mutum da dai sauransu ba. Yace sun gaji bashi sama da nera miliyan dubu saba’ain da bakwai. Yace mafi yawa sun biya.
Dangane da ‘yan kwangila gwamnan yace sai ranar 29 ga wannan watan su bayyana kudin da suke bin gwamnati. Yace babu wanda zai iya ce komi akansu yanzu.