Wani Babban Malami a Qasar Misra yayi bincike sosai akan ZINA da kuma illolin da take haifarwa ga Bil Adama ta fuskar rayuwarsu, kiwon lafiyarsu da kuma addininsu.
Acikin littafin yake cewa:
Duk mutumin daya dauki ZINA ta zama aikinsa na yau da kullum, zai hadu da cututtuka masu yawa acikin zuciyarsa.
Zai zamanto koda yaushe yanajin alamar wata irin QAZANTA tattare dashi.
Kuma koda shi kansa bazai Qirga kansa cikin
mutane masu tsarki ba.
Malamin yace idan MAZINACI ya bunkasa, wani lokacin har yakan ji sha'awar
aikata fasadin da 'yan uwansa Muharramansa irin su Mahaifiyarsa, 'yarsa, yayarsa, Ko 'yar uwar Mahaifinsa ko Mahaifiyarsa.
Sannan yace ZINA tana gurbata Zuriyyar duk masu yinta.
komai dadewa sai kaga wasu daga cikin zuriyyarsu suma sun tsunduma acikin harkar.
Anyi ittifaqi babban abin dayake saurin rufta mutum izuwa zina a wannan lokacin shine kallace-kallacen fina-finan batsa wato BLUE FILM.
Saboda haka matasa maza da mata yanada kyau ku nisanci wadannan abubuwa idan mutum yanada halin aure yayi.
Hakika duk mai hankali da kuma tsoron Allah da kaunar Gamuwa dashi, bazai kusanci zina ba.
Ya Allah ka tsaremu daga gareta.
Ka tsare dukkan zuriyarmu.