Makarantar horar da Limamai, Ladanai da Alkalan gasar karatun Alkur’ani mai girma na kungiyar Izalatil Bidah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), ta yaye dalibai 1,105 tun kafuwarta a 2001.
A jawabinsa wajen bikin yaye dalibai na wannan shekara, Shugaban wannan makaranta, Hafiz Aminu Yusuf ya bayyana cewa wannan yayewa, ita ce ta 15 tun daga bude makarantar, wacce Shugaban majalisar Malamai na kungiyar na kasa, Shaikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya bude don a rinka ilmantar da da Alkalan gasar karatun Al-kur’ani mai girma, da shugabannin makamar, da Limamai da Ladanai.
Ya ce kadan daga cikin manufofin bude wannan makaranta, akwai samun kwararrun Alkalai wadanda za su rinka yin alkalanci a gasar karatun Alkur’ani a dukkan matakai na gasar, karantar mahalarta ilmin tauhidi, ilimantar da tsarin aikin gudanarwa a aikace, ilimantar da Limamai da Ladanai makamar ayyukansu don su jagoranci al’umma a kan ilmi ingantacce.
Daga nan sai Hafiz Yusuf ya’yi godiya ta musamman ga dukkan Malaman makarantar bisa sadaukar da kai da suke yi na karantar da bayin Allah, duk da dimbin ayyukan da ke gabansu, musamman shugaban majalisar Malamai na kasa, Shaikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir.
A jawabinsa, Shugaban Majalisar Malamai na kasa, Shaikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir, wanda mataimakinsa na biyu, Shaikh Sa’idu Hasan Jingir ya wakilta, ya’yaba wa kwazon da daliban suka nuna na jajircewa na tsawon shekaru biyu suna daukar darasi bisa abin da ya shafi addininsu, duk da dimbin ayyukan da ke gabansu.
Shaikh Jingir, ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga al’ummar kasar nan da su dukufa da yin addu’o’i da fatan Alheri ga kasar nan, kuma da samun ruwan sama mai albarka.
Title :
JIBWIS Ta Horar Da Malamai Da Alkalan Gasar Karatun Alkur’ani
Description : Makarantar horar da Limamai, Ladanai da Alkalan gasar karatun Alkur’ani mai girma na kungiyar Izalatil Bidah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), ta...
Rating :
5