ABU TALHATAL ANSARIY (RA) yace:
"Watarana Muna tare da Manzon Allah (saww) awajen wani yaki, Mun hadu da abokan gaba, (Wajen ya yamutse). Sai naji Manzon Allah (saww) yana cewa:
"YA MALIKA YAUMID DEEN! IYYAKA NA'ABUDU WA IYYAKA NASTA'EEN".
WALLAHI NAN TAKE SAI NAGA MAZAJE SUNA ZUBEWA A QAS.. MALA'IKU SUNA SUNA SARANSU TA GABANSU, DA BAYANSU".
- Abu Nu'aym ne ya fitar da Hadisin acikin DALA'ILUN NUBUWWA, hadisi na 386, 459 da kuma na 460.
Ya Allah yi salati ga wannan Jarumin Annabawa, adadin numfashin halittunka, Gwargwadon bayyana da 'buyan darajarsa... Albarkacin salatin, Ya Allah ka fidda komai daga zuciyarmu ka cikata da tsantsar Mahabbatu Rasulillahi (saww).
– Daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP.