Mutane hudu ne suka rasu cikin sa'oi kadan bayan da suka kammala cin abinci da ake zargin amaryar da ba ta son mijinta ta yi wanda kuma ake gani akwai guba a ciki.
Dan uwa ga mutumin nan da ya rasu sakamakon zargin matarsa 'yar shekaru 14 da laifin sanya maganin kashe bera a cikin abincinsa, ya bayyana cewa sun amince da janye zargin da ake yi wa yarinyar bayan da kotu ta umarci biyan diyya.
A cewar Musa Sani da ke zama dan uwa ga Umar da Allah ya yi wa rasuwa, watanni biyu da suka gabata bangaren gwamnati ya tuntubesu kan batun janye zargin Wasila Tasi'u da ake zargi da halaka dan uwansa da sanya maganin kashe bera a cikin abincinsa, abin da yayi sanadin rasuwarsa saboda kyamatar auren dole. Mutane hudu ne dai suka rasu bayan cin wannan abinci cikin sa'oi kadan bayan sun kammala cin abincin.
A cewar majiyar kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP wannan zargi an janyeshi tun a ranar Laraba bayan matsin lamba daga kungiyoyi na masu fafutika duba da karancin shekarun yarinyar, inda su ma a bangaren mamacin daukar nauyin zuwa kotu da zirga-zirga ke zame musu aiki tsakanin garinsu zuwa inda ake shari'ar daga kauyen 'yan soro da ke a jihar Kano.
Ana dai ganin babu hannun masarautar Kano cikin wannan hukunci.
Title :
Janye karar matar da ta kashe mijinta a Kano
Description : Mutane hudu ne suka rasu cikin sa'oi kadan bayan da suka kammala cin abinci da ake zargin amaryar da ba ta son mijinta ta yi wanda kuma ...
Rating :
5