Idan mutum yana cikin yin sahur, sai ya ji kiran sallah yaya zai yi?( Sheikh Abdulwahhab Abdullah)
AMSA: A irin wannan hali mutum zai qarasa abin da ke hannunsa ne. Domin hadisi ya tabbata daga Abu Huraira radhiyallahu anhu ya ce:
''Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce: ﺇﺫﺍ ﺳﻤﻊﺃﺣﺪﻛﻢﺍﻟﻨﺪﺍﺀﻭﺍﻟﺈﻧﺎﺀﻋﻠﻰ ﻳﺪﻩﻓﻠﺎ ﻳﻀﻌﻪﺣﺘﻰ ﻳﻘﻀﻲﺣﺎﺟﺘﻪﻣﻨﻪ Ma’ana: Idan dayanku ya ji kiran sallah alhali qwarya tana hannunsa, kada ya ajiye ta, har sai ya biya buqatarsa .
Amma a nan sai a yi hattara, kada a mayar da irin wannan dabi`a ta zama al`ada a kullum domin ba ance mustahabbi bane yin hakan ballantana a ce ana so a rinqa yi, sassauci ne akayi ga wanda ya fara cin abinci sai lokaci ya kure masa.
wa sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammadin wa ala aa’lihi wa sahbihi ajma’in.