Tambaya:
Malam koya halatta na kalli gashin macen da nakeso in aura ???
Ko kuma don Allah malam ka taimaka kaimin bayanin abunda ya halatta in kalla a jikin macen dazan aura kafin muyi aure.
Nagode.
Allah ya gafarta maka.
(Daga Khamis Abdallah)
AMSA.
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To dan'uwa ya halatta ka kalli macen da kakeso ka aura.
Kamar yadda yazo a cikin hadisi, inda Annabi (s.a.w) yake cewa:
"Idan dayanku yana neman aure, to in yasami damar kallon abin dazai kira shi zuwa aurenta, toya aikata hakan"
Abu dawud a hadisi mai lambata: 2082.
Amma malamai sunyi sa6ani akan wurin daya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da yaje neman aure:
1. Akwai wadanda sukace zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai, saboda tafin hannu yana nuna ni'imar jikin mace, kamar yadda fuska take nuna kyau.
Saboda haka sai a takaita akansu, wannan itace maganar mafi yawan malamai.
2. Nabiyu kuma sukace, zai kalli duk abin yake bayyana a jikin mace, don haka bayan fuska da hannu zai iya kallon duga-dugai da wuya.
3. Malamai na uku sun tafi akan cewa:
Zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya kalleta.
Wannan ra'ayin shine yafi dacewa, saboda ta haka mutum zaisan yanayin matar dazai aura, yadda ya kamata.
Saidai ba'a son yawaita kallon saboda duk abin da aka halatta saboda bukata, toya wajaba a tsaya a gwargwadonta.
Wannan yasa yawaita zuwa zance da yawaita yin waya, zai iya zama haramun saboda yana iya tayar da sha'awa, sha'awa kuwa tana iya kaiwa zuwa barna.
Wal iyazu billa.
Saboda haka matasa ku kula dan kunji ance ya halatta, kada mutum kuma ya wuce gona da iri a wajen kallon.
Mai neman Karin bayani, yaduba:
Al'insaf 8\15 da Muhallah 9\161.
Allah shine mafi sani.