Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce yanason ya ci gaba da jan ragamar kungiyar, duk da cewa ana alakanta Rafael Benitez da maye gurbinsa.
Ancelotti wanda ya kulla yarjejeniyar shekaru uku tare da Real na da sauran shekara daya a kwangilarsa.
Dan Italiyan mai shekaru 55 ya jagoranci Real a kakar wasan da ba ta lashe kowanne kofi ba.
"Ina da kwarin gwiwa na ci gaba da jagorancin kulob din," in ji Ancelotti.
Tsohon kocin Liverpool, Benitez ya yi aiki a karamar kungiyar Real Madrid sannan ya lashe kofin zakarun Turai tare da Liverpool da kuma na Europa da Chelsea.
Title :
Ina son in ci gaba da jan ragamar Real'
Description : Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce yanason ya ci gaba da jan ragamar kungiyar, duk da cewa ana alakanta Rafael Benitez da maye gurbinsa...
Rating :
5