Dangane da fa'idar Hulba wacce muka fada jiya, BANDA MACE MAI CIKI!!!
Bai kamata mace mai ciki ta sha Garin Hulba ko Man Hulba ba, sai dai in nakuda takeyi.
Ita hulba tana motsa Mahaifar mace, tana sanya Mahaifar ta turo abinda ke cikinta ne. Don haka bai dace mace mai ciki ta sha ba, har sai nakudarta tazo.
Amma mace mai shayarwa, ita ce ma tafi dacewa tayi amfani da Hulba domin samun cikakkiyat lafiyar shayarwa, da kuma wadatuwar ruwan nono ga jaririnta.
Matar da take fama da Matsalar Qaikayin gaba, ko Kurajen gaba, ta samu garin Hulba ta dafa ta rika shiga ciki bayan ta surka shi... In sha Allahu zata samu waraka.
Wacce take fama da matsalar Bushewar gaba, idan tana shafa Man Hulba acikin gabanta zata samu yayewar Matsalar.
Hakanan wacce fatar jikinta take yamushewa idan tana shafa man hulba zata samu waraka.
Kamar yadda muka fada jiya, idan mace tana so ta samu ingantuwar Qirjinta, ta rika dafa garin Hulba tana sha da zuma ko Sugar.
Ko kuma ta rika shan Man Hulbar acikin ruwan dumi tare da zuma, kuma tana shafawa akirjinta, in sha Allahu za'a dace.
BISSALAM.