Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Mallam barka da war haka. Ya aka ji da dalibai? Allah ya bada ladan aikin da ake yiwa addini, ya jikan mahaifa. Mallam tambayace nake da ita. Matata ce take da jinnil ashiq. Tana ci min mutunci lokaci lokaci, idan zata unguwa ban isa na hana ta ba. Idan na hana ta fita za ta ce idan ta fita me zan yi? Kuma ta sa kai ta fita din. Akwai lokacin da nace mata in ta fita mala'iku za su tsine Mata, kawai ta kama dariya tana cewa tsinuwa kawai ta fita. Nayi ta hakuri, na kai karar ta wurin magabatan ta amma ta ki denawa fiye da shekara daya. Ga cin mutunci ga shi kuma ban isa na hana ta ba. Saboda haka wataran na gaji, bayan ta gama ci min mutunci tace zata shiga makwabta bayan karfe 10 na dare, nace me zata yo, tace ba komai, nace baza ta ba, tace ban isa na takura mata ba, ta fita ta shiga makwabtan. Daga nan na yanke shawarar kawai na rabu da ita idan gari ya waye. Da gari ya waye na Kira ta nace mata tunda ba zan iya sa ta ko na hana ta ba, ni zan rabu da ita. Na kawo kudi na bata ta ki karba. Na bata takardar ta karanta tace ita bata ga abinda nake nufi ba. Sai na nuna mata dai dai wurin da na yi maganar sakin nace na sake ta saki daya. Sai ta karbi takardar ta yayyaga ta watsar. Aljanunta suka zo mata suka dinga buga ta da kasa suna cewa zasu tafi da ita suna ce min "I hate you".
Ganin Haka naje na daddanne ta, tun da dama in sun kamata haka nake yi mata har sai tayi barci saboda kar ta ji ciwo. Bayan ta farfado sai take cewa wai Ina ganin an binne ta iya kirji wajen wata jar kasa amma na ce na sake ta. To shine naga abun nata kamar akwai matsalar aljanu, shine bayan kwana biyu na ce na dawo da ita. Wasu suka ce ai sakin bai yiwu ba tunda sanda nace na sake ta ba ita bace a wurin, an dauke ta an kaita wurin da aka binne ta. Na ce ko ya yiwu ko bai yiwu ba, ni dai na dawo da ita. To abinda muke so mu sani shine sakin ya yiwu? Saboda mu san cewa saki ya taba shiga tsakanin mu. An taba yi mata ruqya sau daya shekaru 2 da suka wuce, amma har yanzu ta ki ta yarda a kara yi mata, kuma suna bige ta jefi jefi. Na gode Allah ya saka da alkhairi.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah.
Hakika ita shari'ar addininmu na Musulunci tana aiki ne da abinda ya bayyana agabanta Qarara bisa Hujjoji bayyanannu.
Kasancewar Matarka tana nan agabanka Qarara, da kamanninta da hankalinta. Har tana iya gudanar da dukkan mu'amalolin da suka shafeta, to Duk wani sakin da ya afku atsakaninku za'a daukeshi ne amatsayin saki.
Amma bisa wannan bayanin da kayi, sai nake ganin kamar mafi girman laifin awajenka yake. Tunda ka san tana tare da JINNUL ASHIQ, ai bai kamata ka tsaya kana kulata da jayayya har abin ya kaiku ga saki ba. Maimakon haka da ka mayar da hankalinka wajen neman magani agareta da yafi alkhairi gareku kai da ita.
Duk mutumin da aka tabbatar yana tare da shafar Aljanu, ai ba'a neman amincewarsa idan za'a yi masa magani. Don haka kuskure be daga gareka kace wai "Ta Qi ta amince ayi mata magani".
Ka dubi girman hakkinta wanda yake kanka, kuma ka sani cewar mutukar JINNUL ASHIQ yana tare da ita, ba zai taba barinku ku zauna lafiya ba.
Hasali ma ba zai barku ku samu Qaruwa ba. koda an samu juna biyu, zai iya zubarwa kafin ma kusan akwaishi. Kuma ba zaku dena samun matsaloli ba, har sai kun samu galaba akan Aljanin.
Amma sakin da kayi mata yana nan amatsayin saki. Kuma dawowar da kayi da ita, shine yasa ta dawo amatsayin matarka.
ABIN LURA: Wannan mas'alar tana da bambanci da mas'alar Matar da wani aljani yazo mata bisa siffar Mijinta, Harma ya miko mata takarda yace "NA SAKEKI". ita wannan bata saku ba.
WALLAHU A'ALAM.