Wani Alkali a Indiya ya yanke wa daya daga cikin taurarin fina finan kasar, Salman Khan, hukuncin daurin shekaru biyar a kurkuku bayan an same shi da laifin kisan wani mutum a wani hatsarin mota shekaru 13 da suka gabata.
An zargi Mr Khan da kutsa motarsa cikin wani taron jama'a da ke bacci a bakin titin da ke kusa da gidansa a Mumbai, babban birnin kasar.
Wakiliyar BBC a Indiya ta ce Salman ya dage cewa ba shi da laifi, yana mai cewa direbansa za a zarga da laifin domin shi ne ke tuka motar, amma shaidu da dama sun ce ba haka lamarin yake ba.
Alkalin dai ya ce Salman Khan ne ke tuka motar, kuma a buge yake a lokacin da hatsarin ya auku.
Title :
Salman Khan zai yi shekaru biyar a kurkuku
Description : Wani Alkali a Indiya ya yanke wa daya daga cikin taurarin fina finan kasar, Salman Khan, hukuncin daurin shekaru biyar a kurkuku bayan an sa...
Rating :
5