Aminiya: Masu karatu za su so su ji halin da kake ciki a yanzu tun bayan da wadansu ’yan bindiga suka tare motarku a tsakanin Abuja da Lokoja lokacin da za ku je wasa garin Owerri a kwanakin baya, inda kana daya daga cikin mutane biyar da ’yan bindigar suka harba?
Gambo Mohammed: Jama’a Assalamu alaikum, a gaskiya yanzu A lhamdulillahi, a yanzu idan wani ya gan ni ba zai tava tunanin akwai ciwo a jikina ba, ciwon dai da na ji ta dalilin harbin ya warke, abin da ya rage kadan ne, saura karaya, kowa ya san yadda karaya take sai an bi ta a hankali, kuma su likitocin asibitin da suke lura da ni sun ba ni wani lokaci, dalilin da ya sa ban ma fara atisaye ba ke nan, ka ga idan na fara wani abu ya faru laifina ne, sannan kafin in koma buga wasa sai an yi mini d-ray, sannan an ga yanayin murmurewata, duk da haka su ne za su ba ni damar in fara wasa.
Aminiya: A dangane da gasar zakarun Afirka, me kake ganin yake haifar wa Kano Pillars rashin tavuka abin a zo a gani?
Gambo Mohammed: Idan za a tuna a gasar ta bana mun buga wasa na farko da al-Marreck a Sudan, inda na ci kwallo uku, wato a wasan gida da waje ke nan, na ci kwallo daya a Sudan, sannan na taimaka aka ci daya, sannan a Najeriya na ci kwallo biyu, bayan mun kammala wasan ne za a fara gasar Premier a Najeriya, wato a ranar da muka tafi Owerri za mu buga wasa da kulob din Heartland, sai muka hadu da ’yan bindiga har suka harbi ’yan wasanmu biyar, wannan matsalar ta jawo mana givi, saboda kusan mu biyar da muka samu matsala muna cikin ’yan wasa 11 na farko da ake fara wasa da su. A cikin 11 na farko duk wanda ka ga ba a fara wasa da shi ba imma ba shi da lafiya ko ya ji rauni. Ka ga abin ya shafi wadanda suke ba buga mana lamba 5 da 6, sannan wanda yake buga mana lamba 4, shi kadai muke da shi, domin daya ya tafi Nasarawa United, sai ni, kodayake muna da ’yan wasan gaba masu yawa. Duk da cewa an dauko wani Obiazokor dan wasa gaba da kulob din Rangers, amma an rika samun matsala, daga nan ya bar kulob dinmu, mun yi wasan Sudan da shi duk a gida da waje, a lokacin da za a je Moroko kuma sai ba a je da shi ba, idan ka lissafa mu 5 da kuma shi, ka ga mun zama mu shida ke nan a cikin 11 na farko, idan ka cire mutum 6 dole kulob ya samu matsala ko da a manyan kulob da suke kasashen waja ne kuwa. Muna gani yana faruwa da Real Madrid ko Manchester United da sauransu.
Aminiya: Bayan wannan al’amari da ya faru da Kano Pillars, yaya kake hasashen kulob din a nan gaba?
Gambo Mohammed: Wannan al’amarin ya tava mu, amma duk da haka ana iya bakin kokari, sai dai kawai ’yan kallo suna cewa idan babu wane sai su ga kamar za a iya samun matsala, yana faruwa, wurin da wane yake bugawa idan ba ya nan sai ka ga an samu matsala, saboda ka san yadda kowa ya iya wasa daban, yadda wancan zai ba kulob dinsa taimako daban, haka wancan ma, za ka wani yana taimaka wa kulob dinsa da kashi 100, wani kuma za ka samu kashi 60 yake iya bayarwa, ba wai don bai iya kwallo ba, a’a iya ikonsa ke nan. Don haka Pillars za ta ba marada kunya, za mu dawo da zafinmu tun da ka ga a cikin wadanda al’amarin ya shafa ni kadai ne ban dawo wasa ba, ni ma nan ba da jimawa ba zan dawo.
Aminiya: A cikin koci-koci da ka yi aiki da su wanne kafin jin dadin aiki da shi?
Gambo Mohammed: Babu kocina da ban ji dadin aiki da shi ba, saboda duk wanda na yi aiki da shi ya ba ni duk wata dama da ake ba dan wasa, ka ga kuwa babu yadda za a yi in ce na fi son wannan, ko na fi son wancan, babu kocin da na yi aiki da shi aka ce yau na samu matsala da shi ba.
Aminiya: An yi ta kai ruwa rana tsakanin Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) da Stephen Keshi, wanda shi ne ya nada ka Kyaftin din Super Eagles na vangaren ’yan wasan cikin gida, yaya alakarka take da shi a yanzu?
Gambo Mohammed: Na ji dadin aiki da shi, sannan na ji dadin da ya sake zama kocin Super Eagles, musamman ma a baya da aka rika takaddama tsakaninsa da NFF, gaskiyar magana mu ’yan wasan Super Eagles na cikin gida muna son Keshi, ban san ko wadanda suke waje ba, saboda an jima ba a samu kocin da yake ba mu dama kamarsa ba, shi ya ba mu dama muka buga wasanni har aka gan mu a ce dama a cikin gida akwai ’yan wasan kwallo haka? Shu’aibu Amadu ma ya yi haka. Da aka samu takaddamar zai yi ba zai yi ba ba mu ji dadi ba, yanzu da aka daidaita muna cikin farin ciki. Ina taya shi murna. Allah Ya taya shi riko.
Aminiya: A harkar kwallon kafa ta duniya kasar Sifen na daya daga cikin manya kasashen da ke sahun farko, yaya ka ji a lokacin da aka saka wasa a lokacin da Najeriya ta buga wasa da Sifen lokacin gasar Confederation cup da aka yi kasar Brazil a bara?
Gambo Mohammed: Ana ji da kasar Sifen a harkar kwallon kafa a duniya, to amma ita kwallon kafa tana da wani abu, duk lokacin da ka fara buga wasa, wato bayan ka shiga fili za ka manta da komai, koda a tsorace ka shiga za ka daina, idan ma kana ji kamar ba ka da lafiya tuni za ka ware, ni duk lokacin da zan buga wasa ko ma da wani kulob ne nakan sa wa zuciyata cewa, ya zama dole in yi abun da duk wanda ya kalle ni zai ce na yi kokari. Don haka ban ji komai ba, kodayake shiga wasa ya fi wahala a kan idan da kai aka fara buga wasan, idan aka fara wasa da kai komai za a yi zai zo maka da sauki, akan an fara wasa aka sanya ka, wadanda suke ciki tuni jikinsu ya yi zafi, kai kuma sai ka daidaita kanka da su, wani lokacin hakan ba ya zuwa da sauki.
Aminiya: Wane buri kake da shi a harkar kwallon kafa?
Gambo Mohammed: Burina ba wai ni kadai ba duk wani dan kwallo da yake buga wasa a duniya, wannan ya shafi wanda yake buga local league ko league na duniya babu wani dan kwallo da ba ya so a ce ya yi fice a harkar kwallon kafa, kowa fatansa ke nan, ina fatan ni ma nan ba dadewa ba zan cimma wannan burin.
Aminiya: Ka dade da shahara a harkar kwallo a Najeriya, inda wadanda ba su kai ka ba ma sun fita kasashen Turai don buga wasa, me ya hana ka? Ko akwai wani buri da kake so ka cimma a Najeriya ne?
Gambo Mohammed: Ba ni da wani kuduri da nake so in cimma a Najeriya da ban cimma ba, na lashe gasar Premier sau uku, komai sai lokaci ya yi kafin ka samu duk wani abu da kake buri, babu dan wasan da ba ya son buga wasa a Turai, yadda ake wasa a Turai ya bambanta da yadda ake yi a Afirka, kowa yana da burin ci gaba, ina daya daga cikinsu. Babban burina in ga ina buga wasa a Turai.
Aminiya: Wane kulob ka fi sha’awar buga wasa a Turai?
Gambo Mohammed: Kulob din da nake goyon baya shi ne Manchester United, kuma ina da burin in buga wasa a kulob din, amma a yanzu burina in buga wasa a Turai koda kowane kulob ne, wato ba ni da zavi.
Aminiya: Me za ka cewa masoyanka?
Gambo Mohammed: Ina godiya ga masoyana da masoyan Kano Pillars, ban san me na yi musu ba amma Allah Ya dora musu sona, ina sonsu, duk abin da ka sani a rayuwa suna yi mini, suna yi mini addu’a, duk matakin da na taka to masoyana ne suka cicciva ni. Na gode musu. Allah ya saka musu da alheri.
Title :
Halin da nake ciki bayan varayi sun harbe ni - Gambo Mohammed
Description : Aminiya: Masu karatu za su so su ji halin da kake ciki a yanzu tun bayan da wadansu ’yan bindiga suka tare motarku a tsakanin Abuja da Lokoj...
Rating :
5