GORON JUMA'A DAGA ZAUREN FIQHU
Mafiya alkhairin mutane bayan Annabawa (alaihimus salam) Sai Sahabban nan na Annabi Muhammadu (saww).
Mutane ne na musamman wadanda Allah ya zabesu domin su taimaki Fiyayyen Annabawansa wajen isar da Fiyayyen Sako zuwa ga fiyayyar al'ummah.
Mutane ne su wadanda suka bada rayukansu da rayuwarsu da dukiyoyinsu da lafiyarsu da tunaninsu da lokutansu domin daukaka addinin Allah.
Sun sayar ma Allah komai nasu, shi kuma ya saya da tsada, ya basu Aljannah, kuma ya hada musu da YARDARSA. ya yarda dasu, su ma sun yarda dashi. Ita kuwa yardar Allah tafi aljannar ma.
In banda Annabawa (as) babu wani mutum guda wanda ya kai Sahabban Manzon Allah (saww) tsoron Allah da kuma Qokari da tsayawa bisa tafarkin gaskiya. basu tsoron zargin masu zargi.
Babu wani aikin da zakayi a yanzu ka tarar dasu. Sun riga sun tsere maka. Tsakaninka dasu sai dai addu'a da kuma kokarin koyi da irin halayensu da ayyukansu.
Kar ka yarda ka rayu da Qiyayyar Sahabbai azuciyarka. Idan kayi haka ba zaka sadu da Allah lafiya ba.
BISSALAM WANNAN SHINE GORON JUMA'A DAGA ZAUREN FIQHU