Girgizar kasa mai karfin awo 5.2 ta afku a jihohin Sistan da Balujistan na kasar Iran.
Cibiyar nazarin kasa ta jami'ar Tehrain ta bayyana cewa, girgizar mai karfin awo 5.2 ta afku a garin Jabehar dake da tashar jiragen ruwa, wanda kuma ke tsakanin jihohin Sistan da Balujistan na kasar. Kuma girgizar ta afku a karkashin kasa da nisan kilomita 10.
Girgizar ta dauki tsawon saniya 30 tare da kaiwa har nisan kilomita 157 inda kuma an jiyo alamunta a tashar jiragen ruwan Gwadar dake kasar Pakistan.
Ba a dai bayyana ko ta janyo asarar rayuka ko dukiya ba.