««fitowa na 11»»
بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم
Muslunci ya koyar damu komai saidai in mune bamuyi niyyar binciko suba.
Kokuwa bamu da niyyar aiki dasu.
Yanzu dai kai miji, wannan matar daka auro amana ce a wajenka.
1. Kaji tsoron Allah game da lamarinta.
2. Kakula da cikinta.
3. Kabata abinci yadda muslunci yanema a gareka.
4. Ka kula jikinta.
5. Ka suturce mata al'aurarta.
6. Ka kula da makwancinta.
7. Kasamar mata da inda zata riqa kwana.
8. Ka kula da zuciyarta.
9. Kariqa kawar mata da damuwarta da 6acin zuciyarta.
10. Kariqa zama da ita kanajin abin da takeyi dominka.
11. Kabata damar da zata fahimci cewa lallai ita halalinkace kaima halalinta ne.
12. Kabata damar da zataji cewa bayanka babu wani mahaluki a duniya.
Da hakane Annabi (S.A.W) yake cewa:
Mafificinku shine mafificinku ga iyalinsa, nine mafificinku ga iyalina.
Tabbas munga haka a wurin manzon Allah, don har ban-daki yake shiga da iyalinsa suyi wanka tare.
Kai ''MUDI'' sau nawa kuka ta6a wanka da iyalinka ???
Ko babu sunnah anan sai in dare yaraba tukun ???
Annabi har tsere ya riqayi da iyalinsa.
Kaime ka ta6ayi da matarka ???
Annabi har turereniya yakeyi da iyalinsa wurin fita qofa amma bai dauki wannan rashin kunya ba.
Kai ''MALAM MUDI'' tsaya kaji.
Baiwar Allan nanfa tanada hakki a kanka, ka tausaya mata kazamar mata maganin cutar ciki dana zuciya.
Jikinnan nata gaba dayansa halalinka ne.
Kubawa yara lokaci, domin kusami damar tarbiyyarsu cikin tsarin muslunci.
Ka riqa kwantar mata da zuciya har takai ga cewa babu namijin daya kaika a fadin duniya.
Mace idan ka kyautata mata wallahi ko mahaifinta bai kaika daraja ba a wajenta.
Wannan ya sa idan ka quntata mata duk maza suna iya shiga tsinuwarta watama harda mahaifinta nata, domin kaine ma'auni a wajenta !
Haba ''MALAM MUDI'' Mai zaisa bazaka gyara gidanka yadda kowa zai riqa tunanin dan uwansa ba ?
Idan kana waje kaqosa kadawo gida domin kasan kwanciyar hankalinka tanacan, haka ita ma zata qosa kadawo, harma tariqa bugo maka waya don sanin lokacin dawowarka, masamman idan kayi jinkiri.
Kayi qoqari kariqa bata hannu kuna musabaha duk safiya idan tazo gaisheka, ko tazo yimaka rakiya, ko tazo tarbarka.
Yaushe kata6a rungumeta kosai lokacin biyan bukatarka kawai ???
Wasu abubuwan akan barsu da gangan ace wai na kunya ne kar ariqa fadi, wannan yasa naqasa suke tasowa basu sani ba.
Saboda Qauna da soyayya tayi qaranci a tsakanin masoya har takai ga mace bata damuwa, ko mijinta yadawo ko yatsaya acan babu ruwanta.
Domin dawowar tasa da tsayuwarsa duk dayane tunda bakula da ita yake yi ba.
Sai kuma in dare yayi nanne yake tuna karatun Annabi haba ''MALAM MUDI'' adinga adalchi.
Shiyasa Bahaushe da zarar kace wane yana sunnah zai zaice jima'I ne don shi ne kadai karatunsa.
Rayuwar da mace ta miqa wuyanta gaba daya da hidimar mijinta, shima yadauki wannan aikin.
Zakaga yaran gidan sun taso da sanin dabi'un iyayensu, da tsayuwa a duk inda ake tunani da kuma wuce wuraren da ba a son tsayuwa, qarancin qauna sai ya6ata rayuwar aure da dama, ya shiga tsakanin miji da mata, da tsakanin iyaye da 'ya'yayensu.
Allah ya kyauta.
Zamuci gaba daga yadda muka tsaya a darasi mai zuwa.
Insha Allah.