««fitowa na 10»»
بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم
Maigida munfa dawo kanka yauwa.
Meyasa ka buqaci aure ???
Kanada wata manufa ne ko kuwa kawai kaga magabatanka da tsararrakinka ne sunyi kaima kaga yadace ace kanada mace a qarqashinka kamar yadda kowa yake da ita ???
To kafin kafara neman aure, kamata yayi kasami natsuwa kanemi yarinyar kirki, ko a cikin 'yammata nagari ka nesanci guda 3 sune kamar haka:
(1). Tagari ce amma bata sonka.
(2). Uwarta bata da tarbiyar muslunci ko kadan.
(3)Uwar itama tagari ce amma tana nuna maka matsananciyar adawa.
Sannan idan katashi neman aure kasani cewa:
Ko motar da take qarfe wace zaka riqa hawa ta kaika duk inda kakeso a lokacin da kake so dole sai kasamo lafiyayyiya sannan ka koyi yadda ake sarrafa ta, da yadda zaka lalla6a ta harta jima maka sosai.
Dole kariqa kula da ita wajen kwalliyarta da gyaran injinta lokaci zuwa lokaci, gwargwadon yadda wanda yayita ya tsara, kana wanketa kana bata irin man da take sha wanda zai gyara injinta.
Kuma in katashi yin tafiya baka qure maleji ba bare ta makaka cikin daji ko tasaka kayi hatsari da sauransu.
To haka mace take, idan ka aura kaima dole kamiqe da yin wasu hidimomi matuqar kanada buqatar ganin lafiyarta da kwanciyar hankalinka, da zama mai dorewa.
Mace zata riqa yimaka hidima, amma kaima maigida na qwarai akwai naka.
Shin ka auro wace take sonka ?
Domin idan tana sonka komai kakeso zaka samu.
Sannan kaza6o mai tarbiyya mai sanin addini da kama kai, mai kunya, bayan haka sai kafara dorata akan hanyar da kai kake buqata, ta tafi a kanta.
Amma ka fahimci abu guda Daya.
Mace har kullum tana hukunci da zuciyarta ne, tana da tausayi da soyayya da daukan abu mai hatsari a matsayin qaramin abu.
Duk lokacin da zuciyarta ta6aci zata iya yin komai batare da tunanin abin da zaikai ya komoba.
Saboda dogaron da tayi akan zuciyarta, shiyasa komai ilimin mace idan ranta ya6aci ko kuma akayi mata auren dole da ita da watanta duk sammakal.
kenan idan ka auri wace bata sonka, don Allah kayi mata uzuri.
Kayi qoqari qaunarka tashiga zuciyarta tukunna sannan kanemi haqqoqinka daga baya kamar dai sauran mata.
Maigida na qwarai munayi maka zaton aiki da qwaqwalwa samada zuciyarka, kana da qarancin nuna soyayya, da tausayi, ba kamar matarka ba, to amma qwaqwalwarka takan nuna maka me yadace kayi ???
Annabi yayi rayuwar aure shekara 38 yazauna da Khadija shekara 25 ita kadai ce matarsa, dan sauran 13 ne yazauna da mata 9 lokaci guda, har Khadija takoma ga Allah soyayyarta tana bin qawayenta.
Miji na qwarai kenan,wanda yasan darajar mace, yake bata haqoqinta, idan mace tayi aiki da zuciyarta to lallai shi kuma sai yayi aiki da qwaqwalwarsa.
Amma ya dauki mace kamar abin hawa kullum saidai yahau ya more ya sauka ba wani kulawa da ita gaskiya akwai matsala.
Yanzu ya za'a yi kazama maigida na qwarai baka kulawa da jikin matarka ???
Binciken dazamu fara kenan idan Allah ya yarda.
Amma kanemi taimakon Allah, sannan kasami mace ta qwarai, kanemi mai sauqin kai wace zata tafi daidai da buqatarka, sannan kanemi WACE TAKE SON KA, kaza6o mai addini mai son muslunci, ka auro 'yar namiji ba 'yar mace ba.
Sauran kuma kabarwa Allah ikonsa.
Bayannan ka shirya cewa zaka riqa ganin abubuwan da bakaso, amma haka Allah yayita dole sai kayi haquri, karka ta6a saukowa daidai da matsayinta, sai gidanka ya lalace, kullum kariqa cewa ita mace ce kai kuwa namijine to sai a zauna lafiya.
Zamuci gaba daga yadda muka tsaya a darasi mai zuwa.
Insha Allah.