««fitowa na 7»»
بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم
Mace tagari fa tsayayyiya ce, tasan yadda zatayi maganin matsalarta da kanta, a maimakon neman a saketa ko kuwa lallai wata ta fita, zatayi bakin qoqarinta ne domin taga rayuwar aurenta taci gaba ta hanyar warware matsaloli da sa6ani.
Takan jure bushewar zuciyar mijinta, ta daurewa daukar kura kuransa, domin kar gidanta ya6aci.
Mace tagari takan lura da duk canjin da tagani daga mai gidanta, don haka sai tafara binciken yadda zata warware matsalar.
Bana mantawa a rayuwar makaranta nata6a zama da wata 'yar ajinmu wace aka gaya min wani abu maras dadi game da ita, nayi qoqarin 6oye mata, amma da muka hadu saida tagano ni duk kuwa da dariyar dana riqa yi, wannan abu yajawo hankalina na tambaye ta yadda tagane, sai tace min itafa MACE ce kuma tana tare dani, kar nazaci surutu kawai takeyi dani batasan komai daya shafe niba.
Sai nayi mata nasiha akan abinda aka gaya mini.
Don haka nake ganin ba macen da zata zauna da namiji batasan abin da yake sakashi fushi, murna, tunani, sha'awa ba sai bankaura.
Mace tagari takan zauna da maigidanta a lokacin sa6ani don gyara baya, takan manta da MUGWANCIN da yayi mata idan ta tuna da irin wahalhalun da yakeyi da ita da 'ya'yanta, takan gano cewa saki ba shine mafita na farko ba, sai an rasa yadda za'a yi tukun.
Annabi (S.A.W) yana cewa:
أيما امرأة سألت زوجها الطلاق في غير بأس فحرام عليها رائحة الجنة.
Duk macen data roqi mijinta saki haka kurum to qamshin aljanna ya haramta gareta.
Ahmad,Abu Dawoud, Tirmithiy, Ibn Maja da Darimiy suka fitar.
Ya Inganta.
Kaga kenan mace tagari takan nemi sakine a lokacin da kowa ya tabbatar da cutarwar da yake mata, amma ba don kawai tagaji da zama dashi ko batason wani abu da yakeyi ko don yaqi cika mata wani alqawari ba.
Aure sunna ce da Annabawan Allah duk sukayi, ya kamata mugaya matansu suka zauna dasu ???
Bai dace ba kowane mutum ya riqa jin matsolinki da mijinki, sai in abin yafi qarfinki.
Mace tagari mijinta shine komai, koda bai iya soyayya ba.
Bata zama a gabansa ko gefensa saida yardarsa, takan cika da ladabi aduk inda yake, takan nuna masa qauna sosai ta gaskiya ce ko qirqira ce kawai.
Idan zai fita qafarsa-qafarta, idan taji yashigo ta tarbo shi cikin fara'a da annushuwa, nan da nan tafesa turare ta shafawa lallenta mai yafito sosai ta danyi kwaskwarima, ta canja murya tareda yawan murmushi da fari.
Idan zai fita addu'a, in yadawo godiya da murna da farin ciki.
Mace a kullum mai sanyaya raice ba mai jiran a sanyaya mata ba, farin cikin maigidanta shine nata, komai yabata takan gode, ga fadin yi haquri kamar nunfashinta.
Tana fama da baqin ciki amma tayi dariya, tanajin zafin abin da mijin yayi mata amma tayi tunanin yadda zata faranta masa rai.
'YAR UWA IN KINA BIYAYYAR AURE DON MIJINKI NE TO KITSAYA HAR SAIYA GODE, IN KUWA KINAYI DON ALLAH NE TO YANA GANIN ABIN DA KIKEYI BAZAI WATSAR DA AYYUKANKI BA.
Allah kabamu ikon yin amfani da abinda muka karanta.
Sai mun hadu a darasi mai zuwa.
Insha Allah.