Masu ruwa da tsaki a harkar man fetur a Najeriya sun cimma wata yarjejeniya domin kawo karshen matsalar mai da ake fama da ita a kasar.
Hakan ya biyo bayan wani taron jin bahasi da Majalisar Dattawan kasar ta kira yau Litinin a Abuja.
Alhaji Danladi Fasali shi ne sakataren Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya, IPMAN, kuma bayan fitowarsu daga taron ya shaida wa BBC cewa, "Mun zo wannan taro kuma kowa ya fadi korafinsa, inda a karshe aka kafa wani kwamiti wanda zai fara zaman gaggawa domin ya tabbatar da adadin kudin (da dillalan ke bin gwamnati) kuma a tabbatar ministar kudi ta biya."
Alhaji Fasali ya kara da cewa, "A yanzu maganar da nake har an fara lodi a Lagos; mun gaya wa ma'aikatanmu kowa ya je ya dauko kaya kuma masu gidajen mai da suka rufe duk su bude. A Apapa da Warri da Port Harcourt duk ana lodi yanzu haka".
Najeriya ce dai kan gaba wajen samar da man fetur a nahiyar Afrika, sai dai an kwashe fiye da watanni biyu ana fama da karancin man fetur da dangoginsa, lamarin da ke daf da tsayar da ala'amura cik a kasar.
Ana sa ran janye yajin aikin dillalan man fetur din zai kawo karshen matsananciyar wahalar man da kasar ta sami kanta a ciki.
Title :
Dillalan man fetur sun janye yajin aiki
Description : Masu ruwa da tsaki a harkar man fetur a Najeriya sun cimma wata yarjejeniya domin kawo karshen matsalar mai da ake fama da ita a kasar. Hak...
Rating :
5