KASHI NA 1 ( kafin ka soma karanta DARE NA 1 wannan labari yana da matuqar muhimmanci ka karanta shi, idan baka karanta ba baza ka gane ba )
LABARIN FARKO DAGA LITTAFIN (DARE DUBU DA DAYA) kafin daren farko
An rawaito wani labari cewa : akoi wani sarki a qasashen (india da chaina) wanda allah ya bashi (‘ya’ya) maza jarumai guda 2, sunan babban (shaharya’r) karamin kuma (shahi zama’n) kuma masarautar tasa tana da girman gaske.
.
To ananan.. watarana sai wadannan jarumai guda 2 suka gaji masarautar mahaifinsu, kowanne daga cikinsu yana mulkar wani bangare daga cikin masarutar,
To ananan komai yanatafiya daidai – kamar yadda yakamata -har taswon shekaru 20
sai wata rana babban sarkin maisuna (shaharya’r) ya buqaci ganin dan uwansa maisuna (shahizaman) – wanda shima sarkine awani bangare na qasar –
. to sai sarki (shahar ya’r) ya aika wazirinsa zuwa garin dan uwanasa sarki (shahi zaman) ya sanardashi cewa dan uwansa sarki ( shaharyar) yanabuqatar ganinsa…
To sai waziri yakama hanya ya nufi inda aka’aikeshi, kuma ya sanarda sarki (shahi zaman) cewa dan uwansa (sharyar) na buqatar ganinsa, to sai sarki (shahizaman) ya amasa kiran dan uwansa,
washe gari ya shirya ya kama hanya zuwa garin dan uwansa (shaharya’r), bai gusheba yana ta tafiya harsaida ya iso bayangari, sai ya tuna wani abu da yamanta agida (wato tsarabar dayakeso yabawa dan uwansa)..To kawai. sai ya juya ya koma gida saboda ya dauko abunda yamanta…
to bayan ya iso gida sai ya shiga daga ciki, kuma ya isa dakinsa.. to Me zaigani acikin dakinsa.. ? kawai da yashiga daki sai ya iske matarsa tareda baqin bawa akan gado suna rungume dajuna.. sai yace : (a zuciyarsa) yanzu gashi ban bar garinba, amma ga abunda ya faru, to idan nabar garin kuma menene zaifaru kenan ? kawai atake yacire takobinsa yapille musu kayi.. . daganan sai yafita abunsa, ransa abace, yakama hanya zuwa inda yanufa dafarko..
baigusheba yana ta tafiya harsaida ya isa masarautar dan uwansa (shaharyar),, sai sarki (shar yar) yayi farincikin isowar kaninsa sarki (shahi zaman ). kuma yatara (muqarrabansa) da manyan gari saboda tarbar (shahi zaman)..
bayan haka, sai suka zauna tare suna hira cikin annashawa da jindadi, jim kadan sai sarki (shahi zaman) ya tuna abinda ya faru a gidansa kafin iso garin dan uwansa ( wato abinda matarsa tayimasa), atake sai yashiga wani yanayi na bakinciki.. launin fuskarsa ta chanza.. idanunsa suka nuna alama..
To da (shahar yar) yaga haka sai yazaci cewar wataqila saboda barin gida da yayi shi yasa ya shiga wannan yanayi nadamuwa. sai yabar sha’aninsa bayyi masa maganaba..
To dama dagacikin al a’dun AL UMMAR wannan zamani.. idan mutum ya samu kansa cikin damuwa da bakinciki, to zai fita zuwa daji yayi farauta, kokuma yayi tabin namun daji soboda ya kawarda damuwar dake taredashi
to Ananan, bayan wasu yan kwanaki, sai sarki (shaharyar ) ya cewa (shahi zaman) ya (dan uwana) naga jikinka yayi rauni.. launinka ya sauya kamar kanacikin damuwa ? sai (shahi zaman) yacemasa : Akoi qurji a cikin zuciyata (damuwa).. amma yaqi gayamasa abunda yafaru, to sai (shaharya‘r) yacemasa : inaso dani dakai mutafi farauta… wataqila ko damuwarka zatagushe.. ka samu sanyi acikin zuciyarka.? amma sai sarki (shahi zaman) yaqi amincewa dazuwa farautar.. to sai (shaharya’r ) ya kama hanya yayi tafiyarsa, yabar dan uwansa agida…
To dama gidan sarki (shahar ya’r) yakasance mai hawa 2 ne.. kuma (shahi zaman) yana zaune Ahawa na 2.. kuma wurin da yake zaune yana fuskantar wani wuri da Ake shaqatawa (lambu),,
to bayan (shahar yar ) ya tafi farauta yabar dan uwansa agida, (shahi zama’n) kuma shahi zaman din ya kasance yana zaune shikadai, yana tunani, jim kadan sai yaga anbude kofar fadar (dan uwansa), kuma sai yaga matar (dan uwannasa) ta fito tareda (‘yan mata) guda 20 (kuyangun gidan sarki) da kuma samari (bayi) suma su 20 sun shiga wurin shaqatawar, matar (dan uwannasa) tana tsakiyarsu..
bayan sun shiga wannan wuri.. sai suka shiga wurinda ake wanka (semen full – ko – tapki).. sai kowa ya tube kayansa, kayansa, sai matar sarki tacewa daya daga cikin samarin :(ya mas’udu) Sai ga wani baqin bawa matso, sai ta rungumeshi, kuma haka sauran (yan matan) da samari suma sukayi, (ataqaice) an shaqata, an chashe, a cikin wannan lambu harzuwa faduwar rana, Kuma wannan duka yafarune a idon sarki (shahi zaman) yana zaune yanakallo..
da sarki (shahi zaman) yaga haka ya faru a idansa sai yayi mamaki, yace : (a cikin zuciyarsa) : wallahi wannan bala’in yafi wanda akayi agidana, (wato abinda yake nufi : fasadi da akayi a Idansa a fadar (dan uwansa) kuma da matar dan uwannasa. yafi wanda akayi masa a gidansa) wanda shine dalilin kasancewarsa cikin damuwa,
MUHADU ACIGABAN PART 1 DOMIN HAR YANZU BAIKAREBA
Amma pls kusanar dani idan bakwa bukata kuma comment naku shine zai karamin karfin guiwa naci gaba da maxgo muku
naku Aliyu muhammad