To daama dai a gidan wannan attajiri Akoi wani KARE da kuma ZAKARA tareda matayensa guda 50..… To sai wannan mutumi – attajiri – yaji KARE yana qollawa ZAKARA Qira, shikuma ZAKARAN yana chan nesa, sai yaji KARE yake cewa ZAKARA : kai banza kana inane ne ? Jim kadan sai ga ZAKARA ya danno Aguje.. daya isa wurinda KARE ke tseye sai KAREN yace masa : kai kana cikin walwala da jin dadi, ga can maigidanmu yana shirin mutu yanzunnan.. sai ZAKARA ya firgita ya tambayi KARE : me ke faruwane dan allah ka gayamini ? sai KARE ya bawa ZAKARA labarin abunda ke faruwa da maigidansu a cikin gidan… da ZAKARA yaji wannan labari sai yace : Amma wallahi maigidanmu yana da karancin hankali da tunani, (inji ZAKARA) kuma ZAKARAN ya cigaba dacewa : Ni ganinan dabbane, kuma inada mata har guda 50, idan naga dama sai in yarjewa wasu daga cikin matannwa, idan naga dama kuma sai in batawa wasu daga cikinsu rai, kuma in nunawa wasu qauna, wasu kuma in nuna musu qiyayya… inayin abunda naga dama a cikin matayen babu daya daga cikinsu da ta isa tacemini uffan.. Amma maigidanmu kuma matarsa dayace tak, amma ta gagareshi baisan yadda zaiyi da itaba ? (inji ZAKARA yake gayawa KARE), to sai yaci gaba dacewa : Da nine maigidanmu, kawai Abunda zanyi shine : zan samo buulalane, sannan sai in jawo matartawa zuwa daki incemata : tazo daki zan gayamata abunda takeso, sannan bayan mun shiga daki, sai inkulle dakin, inzaro buulalar in ta zabgamata har sai ta tuba ta hakura, ko inkasheta da duuka…
Da wannan mutumi yaji abunda ZAKARA ya gayawa KARE, sai ya dawo cikin hayyacinsa kuma yayi niyyar Aiwatar da Abunda yaji ZAKARA ya gayawa KARE….
To A nan sai (WAZIRI) yacewa ‘yarshi (shahar zad) : wataqila idan Na Aura miki sarki ( shahar ya’r) ya miki irin abunda wannan attajirii ya yiwa matartasa, sai ( shahar za’d) tacewa baban nata (WAZIRI) : To menene wannan attajiri ya yiwa matartasa ? sai baban nata wazir yacemata : wannan attajiri bayan ya gama ALWALA sai ya samo buulala ya boye a cikin daki, sannan sai ya qira matartashi ya cemata tazo daki zai gayamata sirrinda takeso taji, sannan sai yamutu, To ita kuma da taji haka sai ta bishi zuwa daki,
Da shigarsu daki sai ya kulle dakin da kwado, yazaro buulala yayi ta zabgamata ita kuma sai I’hu takeyi har sai da tasuma,
jim kadan Bayan ta farfado sai ta nemi afuwa, To anan sai wannan mutumi -attajiri – ya yafemata, kuma yayi farinciki hakan, sannan sai suka bar daki suka fito waje, inda jama’a suke, sai jama’a sukayi finciki, saboda tubar wannan mata, sannan aka samu zauna lafiya a cikin wanna gida
..
To da (shaharza’d) taji wannan labari da babanta (WAZIRI) ya bata, sai tacemasa : ni duk da haka ban razanaba, babu makawa sai ka Auramini sarki ( shaharya’r).. da WAZIRI ya fahimci haka sai yayi abunda ‘yarshi takeso, ya shiryata zai kaita gidan sarki (shar ya’r)
Bayan (shahar za’d) tagama shiryawa, za’a kaita gidan sarki, sai ta qira kanwarta (dunya za’d) tacemata : idan na isa gidan sarki, zan Aika a kirawo ki zuwa wurina, ke kuma idan kikazo gidan ( fadar sarki ) kika samu sarki, ya gama tarew dani, (ya sadu da ni) kekuma sai ki cemini : ya (‘yar uwata) ki bamu labari mai dadi mana, wanda zai deba mana kewarmu A wannan dare, to ni kuma zan bawa sarki, labaru masu dadi masu ban Al ajabi, wanda A dalilinsa zai daina kashe (mata) insha ALLAHU.
To haka dai (shahar za’d) da kanwarta DUNYA ZA’D suka tsara.. To daga nan sai WAZIRI ya dauki ‘yarsa (shahar za’d) ya kaita gidan sarki (shahar ya’r). da sarki yaga WAZIRI ya shigo fadarsa sai yayi farinciki, kuma yacemasa : shin kazo mini da buqatata ? sai WAZIRI yace : buqatarka ta iso ya maimartaba, bayan haka sai sarki (shahar ya’r) ya shiga gida saboda ya tare da Amariyarsa (shahar za’d)..
to bayan ya shiga wurinta, itakuma sai tasoma kuka, sai ya tambayeta me ya faru? sai tacemasa : Akoi kanwata qarama Agida, inaso in yi mata bankwana ( saboda sarki zai kasheta bayan ya gama biyan buqatarsa) Atake sai sarki ya Aika aka taho da kanwar (shahar za’d) maisuna (dunya za’d).. da (dunya a za’d) ta iso sai ta rungumi yayarta, bayan haka sai sarki ( shahar ya’r) ya tare da Amaryarsa ya kawar da budurcin ta..
To bayan haka sai sarki da amariyarsa (shahar za’d) da kanwarta (dunya zad) suka zauna A wuri daya suna hira, kafin sarki ya bada umurnin kashe (shahar za’d) kamar yadda yasaba..
To anan ana zaune ana hira, jim kadan sai (dunya za’d) tacewa yayarta (shahar za’d) : ya (yar uwata) dan ALLAH ki bamu labari maidadi mana ! wanda zai debe mana kewarmu a wannan dare ? sai (shahar za’d) tace : kamar yadda kikeso haka zanyi, Amma sai sarki mai martaba ya bani izini tukuna,
Dasarki yaji haka sai ya yi farin ciki da jin wannan magana, kuma ya bawa (shahar za’d) izini tasoma bada labari..
Damaa sarkin yana cikin baqin ciki da damuwa, sakamakon abunda yagani abaya game ha’ inci na mata, kuma dama ya rantse sai ya dau mataki, shiyasa ya ke kashe matan gari, kuma bai daina ba harzuwa lokacinda ( shar’zad) tazo
muhadu a part6 anjuma
naku aliyu