To daga nan sai suka fita aboye babu wanda ya sani, basu gusheba suna ta tafiya a cikin dajin allah – dare da rana kwana da kwanaki – Har sai da suka iso kusada wani babban kogi – mai dandanon gishiri – wanda a gefensa akoi wani bishiya da kuma wani dan tapki (qaramin kogi) wanda matafiya suke sha ruwa daga ciki, To sai suka zauna aqar qashin wannan bishiya saboda suhuta bayan sunsha ruwan wannan tapkin.
bayan wani danlokaci – suna zaune sunahutawa – sai suka ga ruwan wannan babban kogi yana tashi sama yana qara (kamar tafasa ), yana kumfa, bayan haka sai ga wani abu baqi kamar hayaqi mai tsayi (kamar polwaya) ya fito daga cikin wannan kogi, kuma ya nufi inda suke zaune, .da suka ga haka sai suka razana suka tsorata suka hau saman wannan bishiyar dan subuya suga ikon allah menene zaifaru ?? jim kadan sai wannan abu da ya fito daga cikin kogi ya canza ya zama wani jibgegen IFRITU (Aljaini), mai tsawo, mai jiki..mai fadin qirj, yana dauke da akwati akansa, To sai IFRITUN ya iso wurin wannan bishiya, ya zauna yabude wannan akwati ya ciro wani kwalba a ciki.. sannan sai ya bude wannan kwalba, sai ga wata buduruwa kekkyawa ta fito daga cikin wannan kwwalba, sai IFRITU ya kalli wannan buduruwa yace : ya gimbiyata, ya sarauniyar mata, wanda na satota ranar bikinta. inaso inyi bacci kadan ya gimbiyata, sai IFRITUN ya daura kansa akan cinyoyinta yayi bacci abunsa,
to bayan IFRITU yayi bacci, kansa akan cinyoyin buduruwar, ita kuma tanazaune aqarqashin wannan bishiya, Bayan wani dan lokaci sai tadaga Idanunta sama takalli wannan bishiya sai taga (shaharya’r) da (shahi zaman) akan bishiyar, sai ta sauqarda kayin IFRITU daga kan cinyoyinta tamike tseye, tayi musu nuni dahannu tacemusu : kusauko qasa kar kuji tsoron wannan aljanin… sai sukacemata : dan allah kiyi mana afuwa bazamu iyaba munatsoro, sai tace : to wallahi idan baku saukoba zan tayarda IFRITU kuma insa yayi muku mummunan kisa, sai sukaji tsoro suka sauko suna karkarwa, bayan sunsauko, sai takallesu tacemusu : Inasokuyi lalata dani, idan kunqi kuma zan tada IFRITU ya kasheku.. sai suka kalli juna suka soma gardama, sai (shahar ya’r) yacewa (shahi zama’n) kai ka somayi, (shahi zama’n) yace : A’A, kai zaka soma, ni ba zan yiba sai kayi…. Suka cigaba da yin gardama agabanta… sai tacemusu : ya naga kuna gardama ? Idan baku matso kunyi abinda Na umurcekuba to wallahi zan tayarda IFRITU ya muku mummunar kisa.. sai suka tsorata sukayi abunda ta Umurcesu dashi (sukai lalata da Ita) . …
To bayan sun gama sai ta Umurcesu da sumike tseye, sai taciro wani jaka daga cikin aljihunta wanda a ciki Akoi zobe guda (daribiyar da sabain) 570… sai tacemusu : ko kun san menene wannan ? sai sukace : A’A… sai tacemusu :
wadannan zobunane kamar yadda kukagani, kuma masu wadannan zobuna dukkansu sunyi lalatadani Alokacinda wannan aljani yake bacci, kamar yadda kukayi, sai ta cigaba dacewa : kuma bayan kowannensu yayi lalatadani sai inkarbi zobensa, sabodahaka kubani zobenku kamar yadda nakarbi zoben sauran mutane.. sai suka bata zobensu… bayanhaka sai tacemusu : kunga wannan Aljani da yake taredani wanda ya kebacci … ya satoni ne Ranar Aurena.. sannan sai ya sakani acikin kwalba.. sannan sai yasaka kwalbar ackin akwati.. sannan sai ya kulle akwatin da kwado (makulli) guda 7.. kuma ya boye akwatin a ckin teku (kogi) inda dan ADAM bazai iya zuwaba saboda kishin kar wani ya ganni. Amma kuma shima baisan cewa su (mata) Idan suka so yin abunda zuciyarsu ta rairaya musu, to babu mahaluqi da zai iya hanasu aikatawa.
To wadannan sarakunan biyu sunji abunda wannan buduruwa ta gayamusu, sai sukayi mamaki matuqa ! sannan sai sukace : Idan ya kasance wannan Aljanine wanda ya fimu iko da mulki.. kuma (‘ya mace) tayi masa abunda yafi wanda akayi mana ! To Ai Namu mai sauqine, kuma wannan abune wanda zai daukemana kewa, tunda an ci amanar wanda ya fimu, To daganan sai suka juya suka koma gida…
KUBIYONI A PART4
mai maxgo muku lbr shine naku ayau da kullum
Aliyu muhammad
Title :
DARE DUBU DAYA DA DAYA (PART 3)
Description : To daga nan sai suka fita aboye babu wanda ya sani, basu gusheba suna ta tafiya a cikin dajin allah – dare da rana kwana da kwanaki – Har sa...
Rating :
5