To Bayan sarki (shahar ya’r) da sarki (shahi zaman), sun isa gida, atake sai sarki (shaharya’r) ya soma daukan mataki gameda wannan al-amari, sai ya pille wuyar matarsa, haka kuma ya kashe dukkan (yan mata) da (bayi) wadanda sukai lalata tareda matartasa a cikin wannan lambu.. sannan haka kuma bai bar ‘yan matan da suke fadarsa ba, sai ya sa aka kashe su gabadayansu, sai aka wayi gari babu ‘ya mace ko daya a cikin fadar sarki (shahar ya’r) duk ya kashesu …
daga nan sai sarkin ya soma kashe matan garin sa daya bayan daya, babu tausayi, To sai Aka wayi gari babu (‘ya mace) buduruwa a wannan Agari, wasu matan sun samu sun gudu wasu an halakasu.
To tundaga wannan lokaci sai (shahar ya’r) ya kasance A kowanne rana yana auro mace ya kawo fadarsa bayan ya sadu da ita sai ya kasheta a lokacin acikin daren, bai gushe ba yana haka har tsawon shrkaru uku..
A dalilin haka sai AL’UMMAH wannan zamani ta firgita ta watse ta shiga wani hali, (yan mata) duk sun kugudu sun shiga duniya…
To ana cikin wannan yanayi, – sarki yana auro mace idan ya biya bukatarsa sai ya kasheta – sai da watarana sarki (shahar ya’r) Ya Umurci wazirinsa da ya nemo masa (‘ya mace) buduruwa saboda ya biya buqatarsa kamar yadda ya saba, kuma ya gargadi wazirin nasa cewar : Idan bai zo masa da abunda yake bukata ba – ‘ya mace – to zai kashe shi,
Daganan sai waziri ya fita ya zagaye gari gabadaya baisamu ‘ya mace buduruwa kodaya ba, sai tsoffin mata… To Dawaziri ya ga haka sai ya tsorata ya shiga damuwa, saboda rashin samun abunda sarki ke bukata ( ‘ya mace ) sai ya razana matuqa..
To bayan haka, sai wazirin ya nufi gidansa yana cikin wani yanayi na firgita da tsoro saboda yasan sarki (shahar ya’r) zai halaka shi babu makawa..
To daama wannan waziri yana da (yan mata) biyu, sunan babar (shahar za’d) karamar kuma sunanta (dunya za’d), kuma (shahar za’d) ta kasance macece mai ilimisosai fiye da yadda ake tsammani… ta karanta littatafai da daama, Ta karanta littatafai masu yawa yawan gaske a bangaren (tarihi) da labarun al’ummomi da sarakuna wadanda suka gabata, da sauransu…. Kuma takarnta littatafai guda 1000 a bangaren tarihin (al’ummomi) dadama da sarakuna, da kuma bangaren (ADABI) dama sauransu..
To bayan waziri ya shigo gidansa – cikin yanayi na razana da firgita – idanunsa sunyi kolla sunyi JA wur. Sai babbar ‘yar sa (shahar za’d) ta fahimci cewar mahaifinta na cikin damuwa, da bakin ciki, To sai ta tambayi mahaifin nata tacemasa : ya baba na ! me ke faruwa ne ? na ganka, cikin yanayi na damuwa da bakin ciki ? sai tacigaba dacewa : masu hikima sukace :
(( قـــــــل لـمـــــــن يـحــمــــل هـــمــــــــا = فــــــــــإن هــمـــــا لا يــــــــــدوم ))
(( مــــــثـــــــــل مـــــــا يــــفنــــي السرور = هــــكـــــــذاتــفــنـــــي الــــهـــمـــــوم))
((duk wanda ke cikin bakin ciki = to bakinciki baya dauwwama))…
(( yadda farin ciki kekarewa = hakama bakin ciki yake karewa))….
Da WAZIRI yaji wannan magana daga wurin ‘yarsa (shahar za’d) , sai ya bata labarin abunda ya faru tsakaninsu da sarki (shar yar) gabadaya, (cewar zai halaka shi idan bai samomasa bukatarsa ba ) , ita kuma da jin haka sai tausayin mahaifinta ya kamata, sai tace masa : BABA dan ALLAH kar ka damu !.. ka Aura min wannan sarki, zan zauna da shi na amince ko inmutu ko kuma inzama garkuwar dukkan mata gabadaya, kuma inzama dalilin kubutarsu daga wannan bala’i da zalunci na sarki (shahar ya’r).
Da baban nata waziri yaji haka sai ya qara razana, ya cewa yartasa – cikin kakkausar muriya – kaai..A’A dan ALLAH kar kisa kanki cikin hadari, ita kuma sai tacemasa : A’A babu makawa sai ka Aura mini shi.. sai yacemata : ya ke ‘yata ina tsoron kar irin abunda ya faru tsakanin (jaki) da (bujimi) da kuma ubanginsu tareda manomi ya sameki… sai (shahar zad) tacewa baban nata : menene ya faru a tsakaninsu ya BABANA ? … sai baban nata wazirin ya cemata : kisani cewa, Akoi wani Attajiri da ya kasance yana da dumbin dukiya da dabbobi da gidaje da sauransu .. kuma yana tare matarsa guda daya tak, da kuma yara.. a wani bangaren kuma wannan mutumi Allah ya bashi Baiwar fahimtar maganar dabbobi..kuma yana rayuwa ne A karkara (qauye)…kuma agidan wannan mutimi Akoi (jaki) da (bujimi),
to ana nan, sai watarana bujumi ya tako yazo wajen makwancin (jaki). da bujumi ya isa inda jaki yake kwance, sai ya ga wurin (makwancin jakin) a share a tsabtace, kuma an yayyafawa wurin ruwa, ta yadda zayyi sanyi za’a ji dadin kwanciya, kuma a cikin kwanon abincin wannan jaki Akoi (HARAWA) da ( WAKE) wanda aka tankade,..
to sai (bujumi) ya samu jaki na kwance yana hutawarsa, babu wani Aiki da yake yiwa ubangidansa, Akodayaushe yana cikin hutu, (saidai wani lokacin ubangidansa yakan yi anfani dashi na wani dan lokaci kadan ..amma mafi yawancin lokaci yana cikin hutune,. sabanin (bujumi) da a kullum noma yake yi babu hutu….
Muhadu a part5 kashina 5
naku aliyu muhammad
Title :
DARE DUBU DAYA DA DAYA KASHI NA (4)
Description : To Bayan sarki (shahar ya’r) da sarki (shahi zaman), sun isa gida, atake sai sarki (shaharya’r) ya soma daukan mataki gameda wannan al-amari...
Rating :
5