wallahi wannan bala’in yafi wanda akayi agidana, (wato abinda yake nufi : fasadi da akayi a Idansa a fadar (dan uwansa) kuma da matar dan uwannasa. yafi wanda akayi masa a gidansa) wanda shine dalilin kasancewarsa cikin damuwa,
To da sarki (shahi zaman) yaga wannan sai hankalinsa ya kwanta, kuncin zuciyarsa tagushe.. soboda yaga cin amana wanda yafi nasa, kuma an yiwa wanda ya fisa mulki da sarauta, Saboda haka yake farinciki,
kuma daama tun lokacinda (shahi zama’n) yazo wajan (dan uwansa) yaqi yaci komai saboda halinda ya samu kansa aciki.. amma bayan yaga abunda yafaru a idansa sai ya koma hayyacinsa yasoma cin abinci kamar yadda yakamata…
To. Ananan sai ga sarki (shahar ya’r) ya dawo daga farauta, sai ya shigo wurin (dan uwansa) suka gaisa, sai (shahar ya’r) ya luura da (dan uwansa) yaf ahimci cewar yanayinsa yacanza, wato yana cikin farinciki da annashwa bakamar yadda yatafi ya barsaba, kuma yaga yanacin abinci kamar yadda yakamata, bayan dafarko yaqi yaci komai..
to sai (shahsr yar) yayi mamaki, kuma sai yacewa dan uwan nasa : kafin intafi farauta naga kamar kanacikin wani hali nadamuwa,To amma yanzu kuma na dawo na ganka cikin fara’a da annashwa ? dan ALLAH ka bani labari menene yake furuwa ?? sai (shahi zaman) yacemasa : zanbaka labarin abinda ya sani cikin farinciki da annashwa.. amma zakayimini afuwa saboda abida zanfada ba zai maka dadiba…. sai (shahar yar) yacemasa : dafarko kabani labarin dalilin kasancewarka cikin damuwa da bacinrai inji tukuna… to sai (shahi zama’n) yacemasa : kasani cewa A lokacin da ka aiko wazirinka zuwa wurina, na shirya na kama hanya har na iso bayangari.. sai nayi mantuwa, atake sai na juya na koma gida saboda indauko abinda namanta, iso wata gida sai nashiga dakina nasamu matata dawani bawa akan gado, suna lalata, Atake sai nacire takobi na kashesu.. to daga wannan lokaci sai na kasance cikin bakinciki da tunani harzuwa lokacinda na iso wurinka, to wannan shine dalilin kasancewata cikin wannan hali na taqaici.. amma abunada ya sani farinciki da annashawa kuma : sai ya bashi labarin dukkan abunda yaga matarshi tayi tareda (yan mata) da (bayi) a cikin lambu a lokacin da ya tafi farauta sai (shahi zama’n) yacemasa : wannan shine abunda yasani farinciki, saboda anci amanar wanda ya fini mulki da sarauta, shiyasa yanzu kaga ban damu ba..
Dasarki (shahar ya’r) yaji wannan labari sai yayi mamaki, amma kuma sai ya nuna rashin yarda da abunda dan uwansa ya fada masa,
To sai ( shahi zaman) ya fahimci cewa dan uwannsa bai yarda dashiba, sai yacemasa : Idan kanaso ka tabbatar dahaka.. to kabada Umurni asanar cewa zakatafi farauta kamar yadda ka saba, Idan aka fitar da dawakai kuma ‘yan rakiyaka suka fito zuwa bayan gari, to kai kuma sai ka lullube jikinka kabatar da kamanni, ka sulale ka juyo ka dawo gida abunka, saboda ka ganewa Idonka abunda zai faru a gidanka, kuma kagayawa wadanda suka rakaka kar kowa ya biyoka a lokacinda zaka juyo ka dawo fadarka
To sai sarki (shahar ya’r) yayi kamar yadda dan uwansa ya gayamasa. ya bada umurni a sanar cewa zaiyyi tafiya, aka fitar da dawakai .. yan rakiya sun shirya sun fito zuwa bayan gari.. kuma sarki yana taredasu.. da Isarsu bayan gari sai sarki ya sulale yajuyo ya dawo gida bayan ya badda kamanni, kuma ya bada umurnin kada kowa yabiyo shi..
To sarki (shahar ya’r) ya shigo fadarsa a boye, kuma ya labe saboda yaga abunda zaifaru, jim kadan sai ga matarsa tafito tareda yan mata da (bayi) an shiga lambu an shaqata an chashe har zuwa faduwar rana, kamar yadda dan uwansa ya bashi labari, Da (shahar ya’r) yaga abunda ya faru sai yarude yarikide ya dimauce.. kuma ya yarda da abunda dan uwansa ya gaya masa
To anan sai (shahar ya’r) ya tuna wasu baitoci ( acikin harshen larabci) kamar
((لا تــأمـــنــنّ إلـــى النســـــــاء وتـــــثــــق بعـــهــــودهـــــنّ))
(( يـبـديــــن ودّا كــاذبــــا والـغـــدر حــــشـــو ثيـــابــهـــــنّ))
((بحـديــــث يــوســف فاعتـبــر ستــراه بعـــض خـــداعـهـــنّ ))
(( أو مــــا رأيـــت أبـــاك آدم خــارجـــا مـــــن أجـلــــهـــــنّ))
FASSARAN BAITOCI :
(Kada ka amincewa mata, kuma kada ka yarda da alqawarinsu)
(zasu nuna soyayyar karya, al halikuwa yaudarace acikedasu))
(Kayi la’akari da labarin annabi yusufa zaka fahimci makircinsu))
(ko bakaga an fitarda Babanka Adama daga aljanna sabodasuba)
Bayan (shahar ya’r) ya ga abunda matarshi tayi sai yacewa (shahi zama’n) yanzu nayarda dakai…. To sai yacemasa :inaso ka tashi dani da kai mubar masarautarmu mushiga yayon duniya ko zamu hadu da wani wanda ya fimu mulki da iko, wanda shima aka yimasa irin wannan cin amana da ha’inci… Idan muka samu wanda aka yimasa haka, to hankalinmu zai kwanta, amma kuma idan bamu samu wani wanda akyi masa hakaba to fa mutuwarmu tafi rayuwarmu anfani, sai (shahi zama’n) ya amincemasa
MUHADU A KASHI NA 3
MAI SHEKO MUKU LBR SHINE
ALIYU MUHAMMAD