"DUK WANDA AKA BASHI ABUBUWAN NAN GUDA HUDU, TO HAKIKA AN BASHI ALKHAIRIN DUNIYA DA LAHIRA:
1. HARSHE MAI YAWAN ZIKIRIN ALLAH.
2. ZUCIYA MAI YAWAN GODIYAR ALLAH.
3. DA JIKI MAI YAWAN HAKURI ABISA FATUWAR BALA'I.
4. DA KUMA MACE (TA KIRKI) WACCE BATTA HAIFAR MASA DA TSORO AKAN KANTA, KO KUMA AKAN DUKIYARSA. (WATO BATA KULA WASU MAZAJEN, KUMA BATA HA'INTARSA ACIKIN DUKIYARSA).
– Imam Tabaraniy ne ya ruwaito daga Abdullahi bn Abbas, daga Manzon Allah (saww)
**********
Dan uwa mai ka fahimta daga cikin hadisin nan? Wanne abu ne yafi sauki samuwa daga cikin abubuwan nan guda hudu?? kuma wannene yafi wahalar samu??
HARSHE MAI AMBATON ALLAH : Mafiya yawan Mutane ayanzu sukanyi kwanaki masu yawa basu dauki Alqur'ani sun karanta ba. Wasu ma sun yin watanni.
Ba zaka ga mutum ya dage da ambaton Allah ba, sai idan ya hangi Wata musibar ta tunkaro shi, ko kuma ya afka cikin matsala.
2. ZUCIYA MAI GODIYA : Mafiya yawan mutane suna cikin ni'ima amma basu ganewa ballantana har su gode ma Allah. Kana da lafiya da hankali, da Imani. Amma ka Qi ka gode ma Allah, wai don bai baka tarin kudi da dukiya da motoci ba!!
3. JIKI MAI HAKURI BISA MUSIBA: Wannan shine mafi wahala agun Mutanen zamanin nan. Zaka ga mutum ko Mura ce ta kamashi sai ya yi ta gaya ma mutane, Ballantana zazzabi, ballantana idan wani ya bata masa rai, koda acikin motar haya ne, ko a kasuwa sai anyi hayaniya dashi.... MAFIYA YAWANMU BAMU DA HAKURI!!!
4. MACE MAI AMANA: Hmmm... Wannan ko ban ce komai ba, dukkanku kuna da bayanin da zaku iya yi akan halayyar Matan zamani.
Dama tun farko ba zasu aureka ba, sai in kana da TARIN NAIRA DA DALOLI!! Babu ruwansu in ma dukiyar al'ummah ka sato ka tara, ko kuma yankan kai kakeyi, ko kuwa 'Dan fashi ne kai... In dai kana da kudi, to kai ne mijin aure!!
Wata zata aureka ne don ta saci dukiyarka, ta zauna akan arzikinka da ita da danginta... Amma SOYAYYARTA TA GASKIYA tana nan akan saurayinta..
Tana gidanka amma kullum tana chatting da saurayinta.. Watakil ma tana biya masa kudin makaranta daga cikin dukiyarka, Watakil ma suna haduwa idan ta fita unguwa acikin Dankareriyar motar da ka siya mata!!!
Addu'ar ZAUREN FIQHU ita ce: Ya Allah ka harshe mai yawan ambatonka, da zuciya mai yawan godiyarka, da jiki mai yawan hakuri bisa jarrabawarka, da kuma Mata masu albarka, masu nagartar fili da boye.
- DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP -