Kungiyar Chelsea ta dauki kofin Premier bana kuma karo na
hudu, bayan da ta doke Crystal Palace da ci daya mai ban
haushi a Stamford Bridge ranar L
Chelsea ta ci kwallo ne ta hannun Eden Hazard a bugun fenariti daf da za a tafi hutu, bayan da James McArthur ya yi masa keta a da'ira ta 18. Chelsea ta dauki kofin bana kuma na hudu a cikin shekaru 11 duk da sauran wasanni uku ya rage a kammala gasar. Kungiyar ta buga wasanni 35 ta lashe guda 25 ta buga canjaras a wasanni takwas aka doke ta wasanni biyu ta kuma hada maki 83. Chelsea za ta buga sauran wasanni uku da suka rage da Liverpool a Stamford Bridge sannan ta ziyarci West Brom daga karshe ta kara da Sunderland a gida.
Title :
Chelsea ta lashe kofin Premier karo na hudu
Description : Kungiyar Chelsea ta dauki kofin Premier bana kuma karo na hudu, bayan da ta doke Crystal Palace da ci daya mai ban haushi a Stamford Bridg...
Rating :
5