Yan uwana masu albarka, Kamar yadda muka shigo wani sabon lokaci acikin wannan Qasa tamu mai albarka, to fa wajibi ne mu sanar da juna, kuma mu Qudurce cewa BUHARI BAI DA IKON GYARA NIGERIA... ALLAH SHINE KADAI MAI IKON GYARA NIGERIA.
Shi kuwa Allah ba ya chanza ma mutane halin da suke ciki, fache har sai sun gyara abinda ke cikin zukatansu...
Ta yaya Allah zai gyara mu, idan har:
- Malamai suna bin son zuciyarsu, su gaya maka Qaulin Allah da Manzonsa abakinsu, amma zuciyarsu fayau babu tsoron Allah... Sai tsoron talauci. Sun sayar da addininsu don neman duniya!!!
- 'Yan kasuwa da masu hannu da shuni basu kulawa da Hakkin Allah acikin dukiyarsu ballantana su taimaki Miskinai da gajiyayyu da marayu, Bassu da wani buri sai burin su Qara tara dukiya ta kowanne hali, Babu ruwansu da fidda zakkah cikakkiya ballantana Sadaka ko taimakon addini..
- Sarakunan Musulunci bassu da wani aiki sai bin ra'ayin Shugabannin Siyasa, Koda kuwa za'a chutar da talakawansu, koda kuwa hakan zai janyo musu fushin Allah Ko zubewar mutuncinsu!!
- 'Yan siyasar Qasarmu zasu iya aikata kowanne irin fasadi don neman Mulki, koda tsafi ne, ko kisan kai, ko cin mutuncin wasu Musulmai masu Mutunci!!
- Ma'aikatan tsaro, har masu aiki a Ofisoshin gwamnati sun halatta ma kansu karbar CIN HANCI DA RASHAWA DA CIN DUKIYAR AL'UMMAH.
- Talakawan cikinmu bassu da wani kyakyawan fata azukatansu, Sai Kiyayyar juna da gaba da munafurci, da ha'intar Juna, da dogon burin mallakar duniya..
- Matasan cikinmu a wasu dattijan, har da matan aure sun halatta ma kansu Zina da Luwadi da madigo da Tsafe-tsafe.. Sun san cewa Allah ya hana. amma ba zasu iya denawa ba saboda shaitan ya Riga ya hallakar dasu.
- Mata suna yawo tsirara-tsirara akan Titun da makarantu, Mazansu da Iyayensu da yayunsu suna kallonsu amma ba zasu hanasu ba... Haba Malam!!
- Dalibai masu neman Ilimin addini dana zamani bassu da burin su taimaki al'ummah da ilimin da suke nema, sai dai burin yadda zasuyi su samu aiki mai MAIKO, su sache kudin al'ummah su gina gida irin na Alhaji wane, su hau mota irin ta Alhaji wane!!!
- Masu sana'ar hannu sun dulmiya kansu cikin ALGUS da ha'inci.
- Kullum muna samun Qaruwar masu arziki acikinmu kamar Yadda muke samun ninninkuwar Mabarata agefen tituna...
- Mun kyale marayun cikinmu, da Miskinai, da nakasassu da masu Qaramin Qarfi.. Bamu kulawa da sha'aninsu ballantana Allah ya kula damu!!!
- Sin don ka bama Gajiyayye ko Mabaraci NAIRA BIYAR KO GOMA KO ASHIRIN, shine irin kulawar da Allah yace muyi musu????
Ina laifi ka bashi abinda zai isheshi yaci abincinsa na yau da gobe da jibi!!!
'Yan uwa mu gyara kanmu, sai Allah ya taimakemu ya Qara ma Shugabanmu Buhari Qarfin gwiwar da zai yi mana ayyukan alkhairi.
Title :
BUHARI KADAI BA ZAI IYA GYARA NIGERIA BA
Description : Yan uwana masu albarka, Kamar yadda muka shigo wani sabon lokaci acikin wannan Qasa tamu mai albarka, to fa wajibi ne mu sanar da juna, kuma...
Rating :
5