Wani Bom ya tashi a Damaturu jihar Yobe a wata tashar mota. Rahotani sun ce wata mace ce 'yar kunar bakin wake ta tayar da bom din a inda ta kashe kanta.
Sai dai babu bayanin yawan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata. Wata majiya tace an killace wurinda da aka kai harin.
Wannan harin yazo a daidai lokacin da sojojin Najeriya ke ikirarin samun nasara akan sansanonin 'yan Boko Haram da ke dajin Sambisa a jihar Borno makwabciyar Yobe wadanda ake zargin irin wadannan hare-hare a yankin.
Source bbchausa
Title :
Bom ya tashi a Damaturu
Description : Wani Bom ya tashi a Damaturu jihar Yobe a wata tashar mota. Rahotani sun ce wata mace ce 'yar kunar bakin wake ta tayar da bom din a ind...
Rating :
5