Mayakan Kungiyar Bokoharam sun yanka mutane da dama a wani kauye da ke arewa maso gabacin Kasar. Majiyar sojojin Najeriya ta shaidawa kamfanin Dillancin Labarun faransa cewa; A ranar juma’ar da ta gabata ne ‘yan kungiyar ta Bokoharam sun yi amfani da adduna wajen yanka mutane 10 a garin Bambola-Kuwada da ke yankin Madagali a jahar Adamawa. Majiyar ta ci gaba da cewa maharan sun kutsa garin ne da misalin karfe 4 na dare a lokacin da mutane su ke bacci, inda su ka fara yi musu yankan rago. Kasantuwar kauyen a killace kuma nesa da wani birni tare kuma da rashin hanyoyin sadarwa, ya sa an sami jinkirin fitowar labarin abinda ya faru a cikinsa.
Title :
Bokoharam Sun Yanke Mutane 10 Da Wukake A Jahar Adamawa
Description : Mayakan Kungiyar Bokoharam sun yanka mutane da dama a wani kauye da ke arewa maso gabacin Kasar. Majiyar sojojin Najeriya ta shaidawa kamfan...
Rating :
5