Akalla mutane 55 Mayakan Boko Haram suka kashe a kauyukan Bale da Kayamla da ke kusa da garin Maiduguri Jihar Borno a arewa maso gabacin Najeriya. Rahotanni sun ce mayakan kuma sun kona gidaje tare da wawuran dukiyoyin jama’a.
Mayakan sun fara kaddamar da harin ne Bale da Kayamla kafin su doshi Maiduguri a ranar Laraba, kamar yadda wasu mazauna yankin suka tabbatar wa Kamfanin dillacin labaran Faransa.
Majiyoyin sun ce kimanin mutane 30 ne aka kashe a Kayamla, sannan 25 a garin Bale.
Mayakan kuma sun kona gidaje kimanin 50 tare da wawurar dukiyoyin Jama’a da suka hada da abinci da dabbobi.
Sojojin Najeriya sun yi nasarar murkushe mayakan a lokacin da suka nemi shiga garin Maiduguri. Ko da ya ke, Mukaddashin Dakaraktan yada labaru na rundunar Sajan kasar, Kanal Sani Usman Kukasheka ya shaidawa RFI Hausa cewa wasu mata ne suka yi kokarin kai harin Kunar bakin wake a Maiduguri.
Kanal Sani ya ce sun yi kokarin shawo kan ‘Yan ta’addan cikin lokaci kankani.
Wasu majiyoyin Soji da mazauna yankin Borno sun ce kimanin Mutane 9 aka kashe a musayar wutar Maiduguri.
Title :
Boko Haram ta kashe mutane 55 a Bale da Kayamla
Description : Akalla mutane 55 Mayakan Boko Haram suka kashe a kauyukan Bale da Kayamla da ke kusa da garin Maiduguri Jihar Borno a arewa maso gabacin Naj...
Rating :
5