Rundunar sojojin Najeriya ta sanarda cafke wani mutum da take zargin shi ne yake baiwa 'yan Boko Haram abinci da man fetur
Sojojin sun kame mutumin ne a wani kauye da ake kira Gabar Shata cikin garin Baga a jihar Borno.
Rundunar sojojin ta dade tana sama mutumin ido amma rundunar bata ambaci ko dan asalin wane wuri ne ba ko kuma sunasa. Rundunar ta sake gano wasu yara mata har su dari biyu da sittin a wani kauye da ake kira Chalawa dake jihar Adamawa. An cetosu ne sakamakon arangamar da sojojin suka yi da 'yan Boko Haram. Wasu maharan sun arce da ciwon harsashen bindiga yayin da wasu kuma suka halaka.
Yanzu dai ana shirin mayar da matan Madagali bayan an tantancesu.Wasu matan sun fadawa sojojin cewa sun gudu ne daga Madagali lokacin da 'yan Boko Haram suka kai masu hari. Daya daga cikin maharan ya rasa ranshi lokacin da suke musayar wuta da jami'an tsaro.
Manjo Janar Chris Olukolade yace daya daga cikin 'yan banga dake taimaka masu ya ji ciwo.Sojojin sun kuma gano makamin da ake kira machine gun da albarusai masu yawa da motocin hawa da babura. Manjo Janar Kolade yace zasu cigaba da yin sintiri a dajin Sambisa saboda zakulo 'yan Boko Haram har sai sun kawo karshensu.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.