Swansea City ta yi rashin nasara a hannun Manchester City da ci 4-2 a gasar Premier wasan mako na 37 da suka yi ranar Lahadi a Liberty Stadium.
Yaya Toure ne ya fara ci wa City kwallo, sannan James Millner ya kara ta biyu a ragar saura minti tara a tafi hutun rabin lokaci.
Swansea ta zare kwallo daya daf da za a tafi hutu, kuma bayan da aka dawo ne Bafetimbi Gomis ya farke kwallo ta biyu.
City ta karasa cin kwallaye biyu ta hannun Toure da kuma Wilfred Bony, kuma da wannan nasarar ta ci gaba da zama ta biyu a teburin Premier da maki 76.
Swansea kuwa da ta yi rashin nasara a karawar tana mataki na takwas da maki 56, yayin da za ta buga wasan karshe da Crystal Palace ranar Lahadi.