Hakika ciyarwa da shayarwa da tufatarwa suna daga cikin hakkin da iyalanmu suke dashi akanmu. Amma shin da wacce irin dukiya zamu ciyar dasu din??
Manzon Allah (saww) ya gaya mana hadisai da dama wadanda suke bayani akan Hatsarin dake tattare da Ciyar da iyalai da dukiyar haram.
Misali hadisin nan na goma acikin ARBA'UNA HADEETH na Imam Nawawy. Acikinsa Manzon Allah (saww) ya gaya mana cewa: "ALLAH MAI TSARKI NE KUMA BA YA KARBA ABU SAI MAI TSARKI".
Awani hadisin kuma ya tsoratar damu cewa: "DUK TSOKAR DA AKA GINATA DA ABINCIN HARAM, T BABU ABINDA YAFI DACEWA DA ITA IN BANDA WUTAR JAHANNAMA".
ILLOLIN ABINCIN HARAM:
********************×*****
Mutukar kana ciyar da iyalanka da kudaden baitul Malin Qasa wanda ka wawure, ko kuma cin hancin da ka karba, to tabbas babu yadda za'ayi Imani da tausayi ya zauna acikin zukatansu.
Duk yaron da aka auri uwarsa da dukiyar HARAM, aka ciyar da uwarsa da dukiyar HARAM, har ta samu cikinsa ta haifeshi, Sannan aka ci gaba da bashi yana ci yana sha, aka tufatar dashi da suturar HARAM, to babu shakka zai yi wuya Tarbiyyarsa ta inganta.
Hadisan Annabi (saww) sun nuna cewa irin wadannan yaran ba'a amsar addu'arsu kamar yadda ba'a amsar Addu'ar iyayensu, Kuma wannan dukiyar haram din da aka ciyar dashi zata ci gaba da yin tasiri acikin sha'anin rayuwarsa ta duniya da lahira.
Sanin haka shi yasa Matayen Sahabbai da tabi'ai sukan yi ma Mazajensu nasiha duk sanda zasu fita neman abinci. Sukan ce musu:
"TO MAIGIDA AYI KOKARI ASAMO MANA ABINCI TA HANYAR HALAL. DOMIN ZAMU IYA JURE MA ZAMA DA YUNWA DA TALAUCI AMMA BA ZAMU IYA JURE MA ZAMA ACIKIN JAHANNAMA BA".
Ina ma, Ina ma Mutanenmu na wannan zamanin (Musamman shugabanni da jagororin al'ummah, da Ma'aikatan Gwamnati) zasu hankalta su kiyaye da wannan nasihar!!
DAGA ZAUREN FIQHU