An sake zaben Sepp Blatter a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, duk da zargin cin hanci rashawar da ake yiwa hukumar.
Kasashen Amurka da Switzerland ne dai ke gudanar da bincike kan zargin da ake yiwa wasu manyan jami'an hukumar da suka ce sun azurta kan su ta haramtacciyar hanya.
Mr Blatter ya sake samun wa'adin shekaru hudu karo na biyar , bayan da abokin karawarsa Yarima Ali bin al-Hussain ya janye daga takarar kafin zagaye na biyu na kada kuri'ar.
Yariman ya samu kuri'u 73 daga kasashe 290 da ke cikin kungiyar, da ya hana wa Mr Blatter samun rinjayen kashi biyu bisa uku da ake bukata don kauce wa zuwa zagaye na biyu.
Wakilan dake halartar taron a Zurich ba su yi wani tafin a zo a gani ba, wasu ma eho suka rika yi bayan nasarar ta Mr Blatter.
Mr Blatter ya ce zai dawo da martabar FIFA, wadda cin hanci da rashawa suka zubar da kimarta
Title :
Blatter ya sake zama shugaban FIFA
Description : An sake zaben Sepp Blatter a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, duk da zargin cin hanci rashawar da ake yiwa hukumar. K...
Rating :
5