Wani Barawo ne yaje gidan wani ALHAJI zai yi sata sai ya tarar da mai gadi a kofa, sai mai gadin ya tambaye meye sunanshi, sai yace sunan sa SALATI sai ya tambayeshi gun wa yazo sai yace gun ALHAJI yazo. Maigadi ya barshi ya wuce, sai ya tarar da ALHAJI a baranda suka gaisa ALHAJI ya tambaye shi sunanshi sai yace sunanshi ALANTA, kazo gun waye? yace ya xo gun HAJIYA . Aka barshi ya wuce ya tarar da Hajiya a falo ta tambayeshi sunanshi yace sunanshi DAMBU. Kawai sai ya shake Hajiya ya kwace gwalagwalan ta, sai Hajiya tayi ihu tace maigida dambu ya shakeni sai barawon ya fita a Guje Alhaji yace ki sha ruwa,tace ba dambun ci ba mutumin daya fita da gudu. Alhaji Yakama ihu yana cewa maigadi kakama alanta, kawai sai yakama rawan alanta alhaji yace ba alantan rawaba mutumin daya fita yanzu. Haba sai maigadi Yakama ihu yana cewa jama'a Ku kama salati,sai jama'a suka kama salati haka barawon nan yatsere da gwalagwalan..