Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, bai wa wata hukumar gwamnati umurnin hana wani ko wata fita kasashen waje ba, ciki kuwa har da jam'an gwamnatin da ta gabata.
Ya ce, jam'ain gwamnatin da ta gabata, cikinsu har da ministoci suna da dama da doka ta ba su a karkashin kundin tsarin mulki su je duk inda suka ga dama.
A saboda haka, sai ya gargadi dukkanin ma'aikatar hukumomin gwamnati da su guji wulakanta wani a filin sauka da tashin jiragen sama, ko kuma duk wani wajen shiga ko fita kasa.
Wannan sanarwar ta fito ne ta bakin babban mai yada labaran Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu.
Ya kuma yi kira da jami'an gwamnati su kiyaye da dokokin kasa tare da bin doka da oda.
Title :
BAN HANA MINISTOCIN JONATHAN FITA KASASHEN KETARE BA -Buhari
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, bai wa wata hukumar gwamnati umurnin hana wani ko wata fita kasashen waje ba, ciki kuwa har da jam...
Rating :
5