Wasu tagwayen bama-bama sun hallaka mutane bakwai tare da jikkata da dama a garin Tashan Alade da ke karamar hukumar Hawul a kudancin jihar Borno.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa BBC cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe shida da rabi na safiyar Jumma'a lokacin da ake taron daurin aure.
Ya ce bam na farko din da aka dasa ya tashi kusa da wani shagon sayar da kaya ne da ke kusa da wajen bikin auren.
Wata majiyar tsaro a Maiduguri ta tabbatarwa da manema labarai afkuwar lamarin, ta kuma ce an cafke wanda ake zargi da dasa bam din.
Garin na Tashan Alade ya sha fuskantar munanan hare-hare a baya bayan nan, da ake dangantawa da 'yan kungiyar Boko Haram.
Title :
Bam ya kashe mutane 7 a Borno
Description : Wasu tagwayen bama-bama sun hallaka mutane bakwai tare da jikkata da dama a garin Tashan Alade da ke karamar hukumar Hawul a kudancin jihar ...
Rating :
5