Za mu fara da jin cikakken sunanka da takaitacen tarihinka?
Farko sunana Adamu Abubakar an haife ni a niger state nayi karatu na duk a niger, kuma ni kabilar nufe ne.
Ina ka samo lakabin Bangis?
Ana kirana Babangida ne sai ni kuma na takaita shi zuwa Bangis don saukakawa.
Wace shekara ka fara harkar waka?
Na fara harkar waka a shekarar 2005, da wakokin turanci yanzu haka na yi wakoki kimanin 60.
Gashi kai ba bahaushe ba me ya baka sha'awar yin waka da yaren hausa?
kasan yaren hausa akwai dadi, kuma ni cikin hausawa aka haifeni kuma cikin su na yi rayuwa, Saboda haka ina sha'awar yaren hausa, wannan ne ya sa.
Wanene ubangidanka a harkar waka?
Ubangida na shine Adam A. Zango Na hadu da shi a yayin da na ke ganiyan shan wahala ina aikin wahala a kaduna, a lokacin idan na yi aikina na kan tara kudi na tafi studio nayi waka, daga nan ya ji wakokina daga nan ya ga eh lallai zai iya tafiya da ni.
Akwai wata wakar ka mai suna shahuda, me ya sa ka yi wannan wakar, labarin da ka bayar a wakar ya faru da gaske ne?
wakar shahuda na yi ta ne kawai kirkira ce, amma bai faru ba. Sai dai idan kunji wakar nasan idan kina da tausayi ko kana da shi za ka so ace shahuda ta auri Mr. Bangis (Dariya)
Wace waka ka fi so cikin wakokinka?
Nafison makosan hausawa wanda na yi da talba, da kuma sangale.
Me nene burin da kake son zama anan gaba?
Inason duniya ta sanni tamkar macheal jackson.
Daga karshe me za ka cewa masoyanka?
Abinda zance da masoyana shine dan adam 9 yake baicika 10 ba, ko da yaushe idan suka ga kuskure a tare dani ko ince damu, a gyaramana kuma Allah yabar zumunci nagode, Kuma inaso masoyana su shiryawa sabon video Album dina mai suna hausa shoki, ya na tafe
Title :
Babban Burina Shine Duniya Ta Sanni Tamkar Michael Jackson- Mr Bangis
Description : Za mu fara da jin cikakken sunanka da takaitacen tarihinka? Farko sunana Adamu Abubakar an haife ni a niger state nayi karatu na duk a nige...
Rating :
5