Duniya ina zaki damu ne? Aure ibadane kuma ðan hakurine, idan anyi hakuri to zaga amfanin yinsa, rashin yin hakuri azaman aure daidai yake da hawa tubalin dana sani.
A wanne matsayi za'a ajiye Rukayya umar Santa (Dawayya)?.
Tayi aure gwanin bansha'awa, anyi shagali a wajan bikin. Auren Rukayya Dawayya anyi shagali fiye da yanda mai tunani zai iya tunanowa, matsawar baije wajen da aka tanaza dan shagalin ba.
Bari muðan gulmata maku abinda ya faru a wajen hidimar bikin, kafin kuji yanda akayi yanzu auren ya mutu.
SHAGALIN AUREN RUKAYYA DAWAYYA.
Auren Rukayya Dawayya ya kafa sabon tarihi a kannywood. Domin anyi shagali kala-kala. Anyi baragaza da dukiya an nuna akwai kuði wajen ango da amarya.
Hotel aka kama a Abuja, aka saye komai na ciki har tsawo sati biyu ana shagali.
Dik abin da zakaci ko zakici, ko kuma na sha, to kyautane har tsawon sati biyu.
Bayan Hotel, an kuma kama wani katon gidan Rawa a Abuja mata da maza sunata baje kolinsu sabida murnar auren Rukayya Dawayya.
A jirgi aka rika ðauko kawayen amarya ana kaisu wajan fati.
Kowacce kawar amarya sai da aka bata wayar salula (Phone), kuma akayi ma su angon biki kyauta, abokan Ango ma haka akayi ma su.
Amarya shigar kaya kala Ashirin tayi haka ma Ango. Ita kanta amarya ajirgi aka kaita gidan mijinta.
Kaðan kenan daga cikin irin shagalin da akayi abikin Rukayya Dawayya.
Amma abin kunya har aure ya mutu, sun Rabu.
Ku biyo mu dan jin yanda aka haihu acikin ragaya.
ZAMAN AUREN RUKAYYA DAWAYYA.
Tabbas Rukayya Dawayya tayi zaman aure agidan mijinta, amma bai wuce zaman shekara ðaya ba kacal.
Ana ðaura auren Amarya da Ango suka tafi kasa mai tsarki (Makka). Sabida Rukayya tanada yan uwa acan.
Acan makka ne Allah yabada Rukayya Juna biyu, ta haifi zankaðeðan jinjiri na miji.akayi biki aka sa mashi suna Arfat.
Aure yana kara danko idan aka soma samin zuri'a.
Amma awajan su Rukayya Dawayya ba haka abin yake ba.
Sabida bayan haihuwarta ne suka rabu hannun riga da mijin, ya sake ta.
Dan jin mai yasa aka saketa ku biyo mu.
DALILIN MUTUWAR AUREN RUKAYYA DAWAYYA.
Sanin kowane aure yanada rai, kuma bisa dogaranmu musilmai dik abinda yake da rai to zai mutu wata rana.
Hakanne yasa muka alakanta mutuwar auren Rukayya da Wayya da cewa wa'adinsa ne ya kare.
Da yake komai yana da sila.
To silar mutuwar auren Rukayya Dawayya tace mijin da aura ne bashi da kirki, kuma ga yawan fishi.daga ta bashi shawara kawai sai yace ya sake ta, ita babarshi ce da zatayi mashi faða, inji tsohon mijinta.
Koma maye ta faru ta kare Allah ya kyauta gaba.
Title :
AUREN RUKAYYA DAWAYYA YA MUTU.
Description : Duniya ina zaki damu ne? Aure ibadane kuma ðan hakurine, idan anyi hakuri to zaga amfanin yinsa, rashin yin hakuri azaman aure daidai yake d...
Rating :
5