BBC ta sanar da 'yar kwallon Nigeria, Asisat Oshoala a matsayin gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta mata a duniya na wannan shekarar.
Oshoala 'yar wasan Liverpool, ta samu kyautar ce bayan da masu sauraron BBC suka zabe ta daga cikin 'yan kwallon mata biyar da aka kebe. Ta doke 'yar Spain Veronica Boquete da Nadine Kessler ta Jamus da Kim Little 'yar Scotland da kuma 'yar Brazil, Marta. Wannan shi ne karon farko da BBC ta karrama 'yar kwallon kafar da ta fi yin fice a wasa a duniya. 'Takaitaccen tarihi' An haifi Asisat Lamina Oshoala ne a ranar 9 ga watan Oktobar 1994 a unguwar Ikorodu ta jihar Lagos.Ta samu kyautar gwarguwar 'yar kwallo a gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 20 a shekarar 2014.Sannan ta kasance 'yar kwallon da ta fi kowacce zura kwallaye a lokacin gasar .An yi ma ta lakabi ba 'Seedorf' saboda irin kwazonta da salon wasanta.A watan Janairun bana, Oshoala ta kulla yarjejeniyar buga kwallo tare da kungiyar mata ta Liverpool.Da farko a matsayinta na Musulma iyayenta sun ki barinta ta murza leda amma daga bisani suka sassauto.
Title :
Asisat ta zama gwarzuwar 'yar kwallon BBC
Description : BBC ta sanar da 'yar kwallon Nigeria, Asisat Oshoala a matsayin gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta mata a duniya na wannan shekarar. Os...
Rating :
5