Ango da amarya da suka fi tsufa a duniya, George Kirby mai shekaru 103 da Doreen Lucki mai shekaru 91 sun amince da daura aure a ranar 13 ga watan Yunin bana.
Jaridar 'Daily Mail' ta kasar Ingila ta rawaito cewa, a shekarar 1988 ne mutanen biyu suka hadu da juna, inda bayan shekaru 27 suka amince da yin aure.
A ranar masoya ta duniya da ake kira "Valetine's Day' ne George ya sanarwa da Lucki cewa yana son ya aure ta.
Da aka yi masa tambayar me ya sa sai yanzu za su gyi auren, George ya bayyana cewa "Ina zaton cewa ban kalli shekaruna ba, kuma yanzu ne lokacin auren ya zo. Doreen tana mayar da ni matashi sabon jini."
Masoyan biyu sun bayyana cewa ba wai za su yi aure ba ne don su kafa tarihi, a a saboda suna kaunar junansu zasu yi.
Title :
Ango da Amarya mafiya tsufa a duniya za su yi aure
Description : Ango da amarya da suka fi tsufa a duniya, George Kirby mai shekaru 103 da Doreen Lucki mai shekaru 91 sun amince da daura aure a ranar 13 ga...
Rating :
5