A Najeriya, wasu kananan sojojin kasar sun yi ikirarin cewa ana sallamar su daga aikin, kuma mai yiwuwa a sallami karin wasu a nan gaba.
Sun dai yi zargin cewa hukumomin sojin na sallamar wasun su daga aikin sojin bisa zargin su da rashin tunkarar mayakan kungiyar Boko Haram a fagen daga a lokacin da 'yan Boko Haram suka kwace garin Mubi, a watan Nuwamban shekarar da ta gabata.Wani soja wanda ya nemi BBC ta sakaya sunansa saboda sha'anin tsaro ya fadi cewa ana korar su ba tare da an basu komai ba.Sai dai kuma sojojin sun yi kira ga shugaban kasa mai jiran gado, Muhammadu Buhari da ya sake yin duba ga matakin da hukumar sojin ta dauka na korar su daga aiki.
Source BBC HAUSA
Title :
Ana korar sojoji a Najeriya - kananan sojoji
Description : A Najeriya, wasu kananan sojojin kasar sun yi ikirarin cewa ana sallamar su daga aikin, kuma mai yiwuwa a sallami karin wasu a nan gaba. Su...
Rating :
5