Kwana guda bayan kotu a Masar ta yankewa hambararren zababban shugaban kasar na farko Muhammad Mursi hukuncin kisa, an zartar da hukunci ta hanyar kisa kan wasu mutane 6 a kasar.
An tuhumi mutanen 6 wadanda mambobin kungiyar Ansarul baitil Makdis ne da laifukan kai hari shingen binciken ababan hawa, da kuma karbar horon ya ki da kai hari da makamai kan jiragen ruwan Masar a arewacin birnin Alkahira.
A ranar 15 ga watan Maris din shekarar 2014 ne aka kai hari shingen binciken ababan hawa na Musturut dake arewacin birnin Alkahira, inda sojoji 6 suka mutu.
A ranar 24 ga watan Maris din shekarar 2015 ne kotun koli ta sojoji ta amince da hukuncin kisa kan mutanen.
Title :
An zartarwa da mutane 6 hukuncin kisa a Masar
Description : Kwana guda bayan kotu a Masar ta yankewa hambararren zababban shugaban kasar na farko Muhammad Mursi hukuncin kisa, an zartar da hukunci ta ...
Rating :
5