Makwanni biyu kenan da fara yi wa mutane kisan gilla a karamar hukumar Takum, jahar Taraba.
Rahotannin dake fitowa daga yankin garin Tumpo a karamar hukumar Takum, jahar Taraba sun bayyana cewa mutane goma sha biyar aka yanka kuma ba'a san ko su wanene suka yanka mutanen da aka tsinci gawarwakin su ba.
Kamar yadda wani mazaunin garin Takum Mr Benjamin Bako ya bayyana, sati na biyu kenan abubuwa makamantan wadannan ke faruwa a yankin kuma hakan ya sa jama'ar garin sun zama kamar masu zama a gidan kaso domin ba su da 'yancin walwala cikin kwanciyar hankali. Kawo yanzu dai gawarwakin mutanen da aka yanka na nan a yashe a dakin ajiyar gawarwaki.
A karin bayanin da mazaunin garin yayi, ya bayyana cewar mutanen da aka yanka masu aikin yankan katako ne daga jahar Nasarawa, kuma akwai Hausawa da Inyamurai da Jukunawa a cikin su. An tare motar su ne mai kirar akori kura sannan aka yanka kusan dukan fasinjojin dake cikin motar.
Haka ma a ranar Lahadin da ta gabata, an yanka wasu mata guda biyar a kusa da barikin sojojin da ke Takum suna kan hanyar su ta zuwa wani taro a wata coci. Shima sarkin fawar Takum Alhaji Ali Sule Paki, ya ce kisan mai kan uwa da wabi! wanda aka soma makwanni biyu da suka wuce basu san abin da yayi sanadiyyar shi ba dan haka abin na da ban tsoro matuka.
Kakakin rundunar 'yan sandan jahar taraba ya bayyana cewar ba'a sanar da shi aukuwar wannan abinda ya faru ba. Kashe kashen wanda yayi kama da na 'yan fashi da makami ya fara aukuwa ne makwanni biyu da suka gabata.
Title :
An Yi Kisan Gilla a Jahar Taraba
Description : Makwanni biyu kenan da fara yi wa mutane kisan gilla a karamar hukumar Takum, jahar Taraba. Rahotannin dake fitowa daga yankin garin Tumpo ...
Rating :
5