Wata kotu a Misira ta yankewa Morsi tsohon shugaban Misira hukuncin kisa a yau.
Kotun ta yankewa tsoho shugaban kasar hukuncin ne a bisa zarginsa da hannu a balle gidan yari da fursunoni suka yi shekaru da suka wuce.
Lauyan Morsi, Abdel-Moneim Abdel-Maqsoud yace za su dakata su ga matsayin da majalisar shura za ta yanke a watan Juni. Sannan su daukaka kara idan ta amnice da hukuncin kisa
A baya dai wata kotu ta yankewa Morsin hukuncin shekara 25 a bisa zargin azabtar da masu zanga a lokacin da yake mulki.
Mohammed Morsi shine zababben shugaba na farko a Misra, sojoji sun yi mi shi juyin mulki a shekara ta 2013.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama na zargin gwamnatin Misira da yin amfani da kotuna don gallazawa Morsi da magoya bayansa.
Title :
An yankewa Morsi hukuncin kisa
Description : Wata kotu a Misira ta yankewa Morsi tsohon shugaban Misira hukuncin kisa a yau. Kotun ta yankewa tsoho shugaban kasar hukuncin ne a bisa za...
Rating :
5