Hukumomin Masar sun kwace kadarorin tsohon fitaccen dan wasan kwallon kafar nan, Mohamed Aboutrika, bayan zarginsa da cewa ya taimaka wa kungiyar 'yan uwa Muslumi, wacce aka haramta da kudi.
A martanin da ya mayar ta shafinsa na Twitter, Aboutrika ya ce ba zai bar kasar ba kuma zai ci gaba da aiki don ciyar da Masar gaba.
Dan wasan, wanda a da yake cikin 'yan wasan kwallon kafa na Afirka da suka fi fice, ya goyi bayan Shugaba Mohammad Morsi lokacin da ya tsaya takara a shekarar 2012.
Gwamntin Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi, wanda ya hambarar da Shugaba Morsi, ta dukufa tana farautar 'ya'yan kungiyar ta Muslim Brotherhood.
Source bbchausa.com
Title :
An kwace kadarorin Aboutrika
Description : Hukumomin Masar sun kwace kadarorin tsohon fitaccen dan wasan kwallon kafar nan, Mohamed Aboutrika, bayan zarginsa da cewa ya taimaka wa kun...
Rating :
5