A karon farko rahotannin da suke fitowa daga arewacin kasar Iraqu sun bayyana cewa an kashe yayan kungiyan nan
ta Boko Haram na Nigeria guda akalla 5 a birnin Musil inda suka je daukar horar soje.
Majiyar Jaridar Premuim Times ta Nigeria ta nakalto daga shafin yanar gizo mai suna Basnews.com yana cewa, wata kungiya mai suna Mosul Youth Resistance Movement ce ta kaiwa yayan kungiyar ta boka haram hari a wata unguwa da ake kira Dargaza a gabacin birnin Musil suka kuma kashe akalla 5 daga cikinsu. Wani mazaunin birnin Musil, mai suna Sa’ed Mamuzini ya fadawa Bosnews cewa mayakan na boko haram sun zo birnin Musil ne don karbar horo soje daga kungiyar ISIL mai iko da birnin sannan hakan ya faru da su.
Title :
An Kashe Yayan Kungiyar Boko Haram A Birnin Musil Na Kasar Iraqi A Karon Farko
Description : A karon farko rahotannin da suke fitowa daga arewacin kasar Iraqu sun bayyana cewa an kashe yayan kungiyan nan ta Boko Haram na Nigeria gud...
Rating :
5