Likitocin Manchester United sun binciki lafiyar Memphis Depay dan kwallon PSV Eindhoven, sun kuma ce zai iya buga mata tamaula a badi.
Dan wasan, mai shekaru 21, zai kammala rattaba hannu a kwantiragin £31m a Old Trafford da zarar an bude kasuwar musayar 'yan wasan kwallon kafa a watan Yuni mai zuwa.
Depay ya buga wa PSV wasansa na karshe a ranar Lahadi, a inda ya yi minti 83 a karawar da suka ci Den Haag 3-2.
Dan wasan ne ya fi cin kwallo a gasar Netherlands, bayan da ya zura kwallaye 22 jumulla, da hakan ya bai wa PSV damar lashe kofin bana, wanda rabonta da shi tun a shekarar 2008.
Title :
An kammala duba lafiyar Depay a Man United
Description : Likitocin Manchester United sun binciki lafiyar Memphis Depay dan kwallon PSV Eindhoven, sun kuma ce zai iya buga mata tamaula a badi. Dan ...
Rating :
5